Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Sojoji Sun Kashe ’Yan Bindiga 14 A Babbar Hanyar Kaduna Zuwa Abuja

Published

on

Rundunar sojin Nijeriya ta kashe ‘yan bindiga guda 14, a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja da kuma yankin Birnin Gwari da ke cikin Jihar Kaduna. Sojoji da ke ‘dibision’ na daya a Jihar Kaduna, sun ceto mutum 31, ciki akwai yara guda 18 da kuma manya guda 13, lokacin da suka gudanar da wanna sintiri.
Wakilinmu ya ruwaito mana cewa, an samu nasarar kashe ‘yan bindigar ne a ci gaba da gudanar da sintirin ‘Operation 777’ wanda ake kai wa maboyar ‘yan bindigan, an dai samu nasarar kwato bindigogi tare da harsasai masu yawa.
An bayyana cewa, bayan ceto mutanen, sojojin sun kwato dabbobin da aka sace a babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja, wadanda suka hada da shanaye guda 49 da kuma akuyoyi guda 42. Za a mika dabbobin ga masu shi bayan an kammala gudanar da binciken masu shi.
Shalkwatar tsaro da ke Abuja, ta tabbatar da aukumar lamarin a lokacin da take yin karin haske ga manema labarai. Ta bayyana cewa, rundunar hadin gwiwa wadanda suka hada da sojojin saman Nijeriya da kuma na ‘yan sanda sun kaddamar da farmaki a maboyar ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane.
Daraktan watsa labarai na shalkwatan tsaro Birgediya Janar John Agim, ya bayyana cewa yankin da jami’an tsaron suka kai farmaki sun hada da dazuzzukan Kamuku, Kuduru, Birnin Gwari da kuma Alawa. Agim ya kara da cewa, sojoji sun kwato bindiga kirar AK-47 guda 18, karamar bindiga guda biyu, wayar salula guda uku da kuma babura guda 32, daga hannun ‘yan bindigan. Ya ce, sojoji guda biyu sun samu raunika, yayin da ‘yan bindigan suka kashe mutum biyu na ‘yan kungiyar sa-kai wadanda suke aiki tare da sojojin a lokacin musayar wuta.
Agim ya ce, “A cikin wannan sintirin dai, an kashe ‘yan bindiga guda 14 tare da kwato dabbobi masu yawa, sannan an samu nasarar ceto mutum 31 wadanda aka yi garkuwa da su da kuma kwato muyagun makamai daga hunnun ‘yan bindigan. An samu nasarar cafke ‘yan bindiga guda biyar tare da wadanda suke taimaka musu mutum biyu, suna kuma taimaka wa jami’an tsaro a kan binciken da suke gudanarwa. Abun takaici kuma, sojoji guda biyu sun samu raunika, inda a halin yanzu suna jinya a asibitin soji da ke garin Kaduna. An kashe ‘yan kungiyar sa-kai wadanda suke taimaka wa jami’an tsaro guda biyu a lokacin da ake musayar wuta da ‘yan bindigan.
“Bari in yi amfani da wannan dama domin in tabbatar wa mutane cewa, rundunar sojoji tare da hadin gwiwar sauran jami’an tsaro za su ci gaba da tsare rayukar ‘yan Nijeriya tare da dukiyoyinsu. Sintirin ‘Operation 777’ zai ci gaba da gudana domin tsare rayuka tare da inganta harkokin ‘yan Nijeriya.”
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!