Connect with us

LABARAI

Talauci Ke Dakushe Kwakwalwar Yara A Makaranta- Bincike

Published

on

Wani sabon bincike ya tabbatar da cewa; talauci yana dakushe kwakwalwar yara a makaranta. Binciken ya ce; yaran da suka fito daga matalauciyar al’umma, inda ake samun iyayensu ba su yi wani karatun kirki ba, kwakwalen yaran na dakushewa daga fahimtar karatu.

Farfesa John Spencer daga Jami’ar East Anglia, a sashen ilimin sanin halayyar dan adam, tare da tawagarsa sun yi nazarin yadda kwakwalwar yara daga watanni hudu zuwa shekara hudu ke aiki wadanda suke rayuwa a kauyukan kasar Indiya.

Bayan sun samu bayanai ne, sai suka kwatanta da yaran da ke zaune a kasar Amurka, inda suka gano cewa; tabbas ‘ya’yan da suka fito daga iyalin da suke fama da talauci, suna fama da dakushewar kwakwalwa.

Har wala yau binciken ya nuna cewa; a duk shekara, yara miliyan 250 da suke fitowa daga matsakaita da kuma matalauciyar kasa, ba su iya cimma muradunsu na ci gaba a rayuwa, kuma hakan yana da alaka da talauci wanda ke dakushe kwakwalensu.

Spencer ya tabbatar da cewa; bincikensu ya tabbatar da cewa; talauci na ba da gudummawa wajen gaza cimma nasara a rayuwa. Amma ya ce; wadansu binciken sun nuna cewa; kwakwalwar wadansu tana aiki har su cimma manufarsu.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!