Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Wani Mutum Ya Kashe Makwabcinsa Bisa Bacewar Wayarsa

Published

on

A ranar Juma’a ne kotun Ebute da ke Jihar Legas, ta bayar da umurnin a ci gaba da tsare Bictor Sunday a gidan yari, sakamakon bugun makwabcinsa da ya yi har sai da ya mutu. Alkali mai shari’a Misis A. O. Salawu ta bayar da umurnin a ci gaba da tsare Sunday a gidan yarin Ikoyi tare da bayar da umurnin mika fayal din shari’ar ga daraktar kungiyar lauyoyi na Jihar Legas domin bayar da shawara.
Sunday mai shekaru 42 da haihuwa, yana zauna ne a gida mai lamba biyar da ke kan titin Balogun cikin Gbara a yankin Lekki, yana fuskantar tuhumar kisa, inda shi kuma ya musanta ya aikata laifin.
Tun da farko dai, lauya mai gabatar da kara Kehinde Olatunde, ya bayyana wa kotu ranar Asabar cewa, Sunday ya aikata wannan laifi ne a ranar biyu ga watan Afriku da misalin karfe 4.45 na asuba, a mahadar Jakande da ke yankin Lekki. Olatunde ya zargi wanda ake tuhuma da yin amfani da karfe inda ya bugi Denir Sapeto dan shekara 55, har sai da ya mutu. “Wanda ake tuhuma ya zargi mamacin ne da sayar masa da wayar salula a inda ya kai caji.
“Amma mamacin ya bayyana masa cewa bai dauki masa waya ba. Sunday ya dauku katotan karfe inda ya dunga buga wa mamacin har sai da ya mutu.”
Lauyan mai gabatar da kara ya kara da cewa, laifin ya sabawa sashi na 223 na dukar manyan laifuka na Jihar Legas ta shekarar 2015.
Kamfanin dillancin labarai na kasa ya ruwaito cewa, sashi na 223 ya tanadi hukuncin kisa ga duk wanda ya aikata irin wannan laifi.
An dage sauraron wannan kara har sai ranar 16 ga watan Mayu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!