Connect with us

WASANNI

Wasan Manchester United Ne A Gabanmu, In Ji Kociyan Barcelona

Published

on

Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Enesto Valverde ya bayyana cewa wasan da zasu buga da Manchester United a gasar cin kofin zkaarun turai shine a gabansu kuma yasa yayi canje canjen ‘yan wasa a wasan da suka buga 0-0 da kungiyar Huesca a gasar laliga a ranar Asabar.

Dan wasa Leonel Messi yana daya daga cikin ‘yan wasan da basu buga wasan ba bayan da yaji ciwo a hancinsa a wasan da suka na farko a Old Trafford bayan wata haduwa da sukayi da dan bayan United Chris Smalling.

Kociyan na barcelona yace lokaci yayi da zai bawa ‘yan wasansa hutu domin tun karar kalubalen dake gabansu na buga wasa da United kuma yana fatan zasuyi kokarin ganin sun samu nasara a wasan da zasu fafata a gobe Talata.

“Mu na sane mu ka saka matasan ‘yan wasa wasu ma basu taba buga wasa ba sai yau duka saboda muna tunanin wasanmu da Manchester United saboda muna bukatar mu mayar da hankali a wasan” in ji Valverde

Ya ci gaba da cewa “Sun gama shiryawa tsaf domin karbar bakuncin United din kuma yana fatan hutun daya bawa ‘yan wasan zasuyi amfani dashi wajen ganin sun samu nasarar zuwa mataki na gaba ta hanyar doke Manchester United din wadda ake ganin tana yawan samun nasara a wasanninta na waje.

A gobe ne dai kungiyoyin biyu zasu kece raini a filin wasa na Nou Camp dake kasar Sipaniya kuma a wasan farko da aka buga Barcelona ce tasamu nasara daci 1-0 yayinda kociyan Manchester United ya bayyana cewa zasu iya doke Barcelona har gida kamar yadda sukayiwa Jubentus da PSG.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!