Connect with us

WASANNI

Wasanmu Da Ajax Ba Mai Sauki Ba Ne – Allegri

Published

on

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Juventus, Madimiliano Allegri, ya bayyana cewa rashin nasarar da kungiyarsa tayi a gasar siriya A a hannun kungiyar kwallon kafa ta SPAL laifin sane saboda shine ya ajiye da yawa daga cikin ‘yan wasan kungiyar a benchi.

Juventus tayi rashin nasara daci 2-1 a wasan da suka kai ziyara kungiyar SPAL kuma kafin a buga wasan Juventus tana bukatar canjaras kawai wanda zai bata damar lashe gasar siriya A karo na takwas a jere.

Dan wasa Kean ya fara zurawa Jubentus kwallo a raga a daidai minti na 29 da fara wasan sai dai daga baya kuma dan wasa Kebin Bonifazi ya farkewa kungiyar SPAL kafin daga baya kuma Sergio Floccari ya zura kwallo ta biyu a ragar Jubentus din.

“Mun so mu gama gasar Siriya A yau saboda komai zai koma mai sauki a wajenmu amma bamu samu dama ba amma kuma matasan ‘yan wasan mu sunyi kokari domin kusan duk abinda aka sakasu sunyi” in ji Allegri

Yaci gaba da cewa “Yanzu wasan kofin zakarun turai shine a gaban mu domin muna da wasa mai zafi a gabanmu wanda yake bukatar dagewa da kuma jajircewa saboda zamu buga wasa da babbar kungiya mai tarihi a gasar”

A wasan na SPAL dai da Juventus ta buga ‘yan wasa tara kociyan ya canja daga wadanda ya buga wasan Ajax na farko dasu sai dai yace wasan Ajad yanada muhimmanci sosai shine yasa ya ajiye wasu daga cikin ‘yan wasan nasa fitattu.

A wasan dai dan wasa Andrea Barzagli ya bayyana yin ritayarsa daga buga kwallo bayan ya buga minti 81 a wasan inda yace lokaci yayi daya kamata ya ajiye takalminsa domin yabawa wasu dama.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!