Connect with us

NAZARI

Yaki Da Taddanci: Bayar Da Hadin Kan Kafafen Yada Labarai Ya Na Da Mahimmanci

Published

on

Alumomi da dama a shekarun da suka gabata sun taka muhimmiyar rawa wajen yaki da ta’addancin da ya addabe su.
Sakamakon ayyukan ta’addanci da ya zamo ruwan dare a cikin wasu alumomi, taddancin ya janyo raba dubban alumomin da iyalansu, inda hakan kuma ya jefa rayuwar su a cikin kuncin rayuwa wasu dubban iyalai suka rasa rayukansu, kafin sojoji su kawo dauki akan lamarin.
A yanzu an samu sauki akan lamurran da aka zayyana a sama saboda jajircewa jami’an tsaro na daukin da suka kawo akan lokaci, musamman jami’an soji.
Rahotannin sun bayyana cewar, sojojin sun samu gagarumar nasara a yanzu, wajen rage ta’addanci da kuma wanzar da zaman lafiya ta hanyar nuna kwarewar su.
Wasu masana suna da yakain cewar, tuni jami’an soji sukaci galaba akan ayyukan da yayan kungiyar Boko Haram suke aikatawa, mussaman a yankin Arewa Maso Gabas, inda hakan ya sanya yayan kngiyar da dama suka arce don boye wa.
Wadannan gungun na yan ta’addar sun hada harda kwararrun masu sace mutane, miyagun yan fashi da makami da suka jima suna cin karen su babu babbaka musamman akan manyan hanyoyin dake cikin Nijeriya.
Sai dai a yanzu, daukacin wannan nau’ukan na ta’addanci dake aukuwa, sai kara zamowa tarihi suke yi a Nijeriya.
Yadda lamarin tsaro yake a yanzu a kasar nan, za’a iya cewa an samu sa’ida, musamman idan akayi dubi da yadda lamarin na tsaro ya yi mummunan tabarbarewa daga shekarar 2013 zuwa shekarar 2015, musamman a yankunan da ta’adancin yafi munana.
Wadanan shekarun, saboda rashin tsaron an dakilewa dubban alumomin da yakunan da ta’addancin yafi munana amfana da ababen more rayuwa, gazawa wajen daukar dawainiyar kula da iyalansu, yancin gudanar da ibadar su da kuma samun yin walala a yankunan nasu kamar sauran yan uwansu yan Nijeriya.
Alumomin da ta’addancin yafi munana a yankunan su, a gaban su ake kashe dubbn yanuwan su da kuma iyalansu.
Idan har sojojin suna son suci nasara wajen magance ta’addanci, tabbas suna bukatar hadin kai, goyon baya da kuma ba wai kawai fahimtar juna daga alummar kasar nan ba harda na kafafen yada labari.
Har idan sojojin suna son su cimma nasarar yakin da ta’addancin, ya zama waji su faro daga sama zuwa kasa akan tsarin baki daya.
Kafafen yada labaran kamar wata Cibiya ce, kuma sune sukafi chanchanta wajen bayar da gagarumar gudunmawa da goyon baya wajen ragargaza yan ta’addar.
Har ila yau, kafafen yada labaran zasu kuma iya karawa sojojin kwarin gwaiwa wajen yaki da yan ta’addar yadda ya dace ta hanyar basu sahihan bayanai don tarwatsa kudurin yan ta’addar ta hanyar kin yada hare-haren yan ta’addar.
Baza’a iya cimma nasarar yaki da yan ta’addar ba dole sai da goyon baya da kuma hadin kan kafafen yada labarai.
Akwai wani abokin aiki na ya nuna jayayya akan amincewar sojijin na yin aiki kafda da jafada da jafafen yada kabaran domin wasu mutane a cikin sojoji mai yuwa suki amincewa da wannan ra’ayin.
Hakika, idan jami’an na soji suka janyo kafafen yada labari a cikin irin wannan yakin da ta’addancin, yanada mahimmanci gaske.
A rubuce yake irin wannan yakin da ta’addancin ana cin nasara ne ta hanyar yin amfani da kafafen yada labari, musaman irin goyon baya da hadin kai da ya kamata kafafen su baiwa jami’an soji.
Kafafen yada labaran basa wuce makadi da rawa wajen dakushe karkashin sojojin wajen yaki yan ta’addar haka zasu dode dukkan kafar da zata karawa yan ta’addar kaimi wajen aikata ta’addancin su akan alumomi.
A saboda hakan ne, wannan marubucin yake da ra’ayin cewar, yadda sojojin suke magance lamarin ta hanyar hadin kan kafafen yada labarai, abin yabawa ne.
Hukumomin na soji sun dauki lamarin da mahimmancin gaske kamar yadda daukacin mahukuntan na soji a yanzu suke kula da lamarin.
A satin da ya gabata mahukuntan sojin sun shiryawa wasu kafafen yada labari taron bita akan wannan lamarin a jihar Kaduna kuma sakamakin taron ya haifar da da mai ido.
A jakabin sa a gurin taron bitar na kwana biyu, Ministan tsaro Mansur Dan Ali an shirya taron ne don baiwa mahalartan sa damar tattaunawa akan akan bukatar ayi na goyon baya da kuma hadin kai a tsakanin sojojin da kafafen yada labarai.
Taron ya kuma samu halartar kawarru daga ko wanne bangarorin biyu harda sanannen dan Jaridar nan Malam Mahmud Jega, da wasu masu tace labarai da suka fito daga bangaren kafaen Talabijin da Radiyo kuma manyan jami’an soji suma ba’a barsu a baya ba.
Taron yazo a daidai kan gaba idan akayi la’akari da irin dimbin mahimmancin da yake dashi ga Nijeriya da kuma yadda lamarin yake ci gaba da jan ra’ayi kuma an wasa kwakwalwa sosai akan lamarin a gurin taron da aka shirya shi musamman don tattaunawa akan dangartakar dake tsakanin sojoji da kuma kafafen yada labaran.
Idan akayi la’akari da irin gayon bayan da kafafen yada labaran zasu taka, hakan ya tunasar da marubucin akan rawar da manyan shugabanni a kafafen yada labari da kuma masu dauko masu rahotanni ake sa ran suma zasu taka akan kakarin da Gwamnatin Tarayya da kuma mahukuntan soji wajen kawo karshen sukkan nau’ukan aikata ta’addanci a Nijeriya.
Acewar mahukutan na soji, kafafen yada labari sune ya dace ace suna akan gaba wajen ilimantar da alumma akan nasarar da sojojin suka samu da kuma dakile yada labaran kanzo Kurege don karawa sojojin karsashi wajen gudanar da yaki da yan ta’adda a Nijeriya.
Mahukuntan na soji sunyi imani cewar, yada labaran na kanzon Kurege da rashin jin ta bakin daya bangaren, ba wai kawai yana da hari bane harda dakile karsaahin sojojin dake yaki da yan ta’addar kuma hakan, zai iya janyo babbar annoba akan yakin da yan ta’addar, domin a baya uein wadannan rahitannin na kanzon kurege sun janyo dakushe karsashin sojojin kamar yadda sojojin suka nuna.
A saboda hakan ne da kuma sauran abubuwan ya sanya wannan marubucin ya fara nasa yin gangamin don baiwa sojojin goyon baya tun a shekarar data gabata.
Rubutu na akan wannan lamarin musamman akan goyon bayan da kafafen na yada labari ya kamata su baiwa sojojin, an wallafa a cikin watan Nuwamba da watan Disamba a shekarar data gabata a jaridar Daily Trust da kuma jaridar Pilot.
A cikin rubutun nawa, na goyi bayan ra’ayin Shugaban hafsan sojoji shi kan shi ya fada da kuma ra’ayin tsohon kakakin rundunar soji ta kasa Bigediya Janar Sani Usman akan cewar, rundunar soji ta kasar nan suna bukatar goyon bayan kafafen yada labarai da kuma na alummar gari don samun nasara akan ci gaban da akeyi na yaki da ta’addanci domin goyon bayan, zai kara karfafa karkashin sojojin dake yaki da yan ta’addar.
Ganin cewar a yanzu ma’aikatar yada labari ta kasa ta fara nata gangamin akan lokaci don amfannin alummar kasa, ya kamata kafafen yada labari su rungumi kalubalen ta hanyar nuna kwarewa wajen yada labaran su.
Alummar gari suma su nuna fahimta sosai da kuma bayar da hadin kai ga sojojin don su samu galaba akan yaki da ta’adsancin.
Anyi gumurzu sosai musamman a lokacin shugabancin hafsan hafsoahin soji Chief Janar Buratai.wajen nuna hazakar sa da kuma kwarewar sa ta dabarun yaki wajen yaki da yayan kungiyar Boko Haram
Kafin Janar Buratai ya karbi ragamar shugabancin, lamarinbna ta’addanci ya munana matuka,inda sakamakon kokarin da jami’an sa suka yi musamman a yankin Arewa Maso Gabas alummar yankin sun samu sa’ida.
Hazaka da kwarewar Janar Buratai, ta fito fili a shekarar 2015 bayan da ya dauki kwararan matakai na kwarewa akan harkar yaki kuma a bisa bin dokokin gidan soji a dukkan aikin da jami’ansa suka fita na yaki da yan ta’adda.
Baya yin sako-sako akan abinda ya shafi yin da’a a tsakanin jami’an sa akoda yaushe da dagewar zaratan mukarrabansa da kuma yadda jami’an da ake turawa gudanar da ayyuka na musamman na yaki da ta’addanci kamar na shirin Lafia Dole da sayran su a shekaru da dama da suka shige hakan ya sanya Janar Buratai ya samu gagarumar nasara da kowanne dan kasa ya tabbatar da hakan ba tare da wata tantama ba.

Ibrahim Biu ya rubuto ne daga Abuja.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!