Connect with us

LABARAI

‘Yan Nijeriya Na Shan Bakar Wahala A Mulkin Buhari, Inji Omotola

Published

on

Fitacciyar ‘yar wasan kwaikwayon Nollywood, mai suna Omotola Jalade, ta caccaki salon mulkin Shugaban Kasa Buhari, inda ta ce ‘yan Nijeriya na shan bakar wahala a mulkin Buharin, sannan ta koka da kashe-kashen da ake a wasu sassan kasar nan.

Omotola ta bayyana hakan ne a shafin sada zumuntar ta, wato a shafin Tuwita, in da take kokawa da kashe-kashen mutane da basu ji, basu gani ba da jami’an tsaro suke yi a matsayin abun takaici, sannan ta ce in gwamnatin Buhari ba ta yi maganin abun ba, zai iya haifar da wata muguwar matsala.

Jarumar ta bukaci gwamnatin Buhari da ta yi wani abu, kan halin da kasar nan ke ciki, in har da gaske tana son ci gaban kasar nan, in kuma ba haka ba kasar za ta fada cikin wani hali.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!