Connect with us

WASANNI

‘Yan Wasana Su Na Cigaba Da Gogewa, Cewar Kociyan Arsenal

Published

on

Mai koyar  da ‘yan wasan Arsenal, Unai Emery, ya bayyana cewa ‘yan wasansa suna cigaba da gogewa a wasanninsu na waje da suke bugawa duk da sukar da kungiyar take sha a waje magoya bayanta na cewa bata kokari idan tana buga wasa a waje.

Arsenal dai ta samu nasara a wasanni biyar cikin wasanni 15 data buga a baya kuma wasanni uku acikin biyar din data samu akan kungiyoyin da suke kasan teburin gasar ta firimiya ne hakan yasa da yawa daga cikin magoya bayan kungiyar basa jin dadi.

Arsenal dai tayi rashin nasara ne kawai a wasa daya a gida a gaba daya wannan kakar kuma Liverpool da Manchester City ne kawai suke da wannan tarihin a kakar bana sia Arsenal sai dai kociyan yayi kira ga ‘yan wasan kungiyar dasu dage domin fara samun nasara a wasannin waje.

“Ina ganin kamar muna nuna gogewa da kwarewa musamman ganin yadda muke samun nasarori sannan kuma ana samun gogewa  a tsakanin ‘yan wasan saboda haka nan gaba kadan komai zai canja” in ji kociyan na Arsenal dan kasar Sipaniya

Yaci gaba da cewa “Muna da wasanni masu zafi a gabanmu kuma suma ragowar kungiyoyin da muke fafatawa suna da wasanni masu wahala sai dai abinda yakamata muyi shine kawai mu mayar da hankalinmu akan samun nasara a wasanninmu”

A wasanni biyu na farkon fara firimiya dai Arsenal tayi rashin nasara a wasannin sai dai daga baya kuma kungiyar sai da tayi wasanni 22 batayi rashin nasara ba kuma a halin yanzu suna fatan kammala kakar wasa a matsayi na hudu ko na uku.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!