Connect with us

LABARAI

Abinda Ya Jawo Yara Miliyan 10 Ba Su Zuwa Makaranta A Nijeriya – Adamu Adamu

Published

on

Ministan ilimi a Nijeriya, Malam Adamu Adamu, ya bayyana cewa, babban dalilin da ya jawo adadin yara sama da miliyan 10, wadanda babu su a jerin masu zuwa makarantun firamare da sakandire a fadin tarayyar Nijeriya.
Ya yi wannan bayanin ne a sa’ilin da ya ke jawabin bude taron karawa juna sani, wanda hukumar ilimin bai-daya (UBEC) ta shirya a birnin tarayya Abuja, domin sarakunan arewacin Najeriya dangane da matsalolin da ke jawo zuwan yara makaranta, wanda a shekarar da ta gabata ya bayyana cewa adadin ya karu zuwa miliyan 13.2.
Ministan ilimin, wanda babban sakataren ma’aikatar, Sunny Echono, ya wakilta, ya shaida wa manema labarai kan cewa, a taron da ya gudana ranar Juma’a muhimman dalilan da su ka jawo hauhawar adadin miliyoyin yara da ba su zuwa makarantar su ne talauci, tashe-tashen hankula da jahilci a bangaren iyaye da makusantan yaran, ko-in-kula daga shugabani dangane da munin abin da kuma al’adu. Sauran su ne, nisa tsakanin makaranta da muhalli, lalurar nakasa, sa yara aikin da ya fi karfinsu da kaura tare da maraici.
Haka zalika kuma ya bayyana yankunan da wannan matsalar ta fi ta’azzara ta yawan kananan yaran da ba su zuwa makaranta da cewa su ne, Kano, Akwa Ibom, Katsina, Kaduna, Taraba da Sokoto. Sauran su ne, jihohin Yobe, Zamfara, Oyo, Benue Jigawa da Ebonyi.
Adamu Adamu ya ce, “ta bangarenmu, a matsayin mahukunta, babban nauyin da ya hau kanmu shi ne abu guda biyu; mu yi kokari wajen samo sahihan bayanai kan hakikanin yawansu da kuma lalabo hanyar da za mu yi amfani da ita wajen rage adadin, zuwa kasa sosai.”
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!