Connect with us

LABARAI

Adadin Masu Anfani Da Intanet A Nijeriya Ya Kai Miliyan 114.7 – NCC

Published

on

Hukumar sadarwa ta kasa wato ‘Nigeriann Communcations Comission’ ta bayyana cewa, masu anfani da intanet a Nijeriya ya karu zuwa adadin mutum miliyan 114,752,357.
Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin rahotonta na wata-wata na masu anfani da kanfunnan sadarwa da ta fitar a ranar Litinin.
Kididdigar ta su ta watan Febrairu ta nuna cewa, an samu karin masu anfani d aintanet a Nijeriya daga adadin mutum miliyan 113,875,204 zuwa miliyan 114,752,357, wanda hakan ke nuna an samu karin sabbin masu anfani daintanet a kasar dubu dari 850,153.
A bisa kididdigar, kanfanin Airtel da MTN na kan gaba wurin samun sabbin kwastomomi, inda kanfanin 9mobile da na Globacom suka fi faduwa.
Kididdigar ta nuna cewa, Kanfanin MTN ya samu karin dubu dari 607,462 a watan, inda ya maida adadin masu anfani da su zuwa miliyan 45,538,633, sabanin na baya miliyan 45,931,171 a watan Janairu.
Kanfanin Airtel shi ne yazo na biyu, inda ya samu sabbin masu anfani dubu dari 430,990 a cikin watan, wanda hakan ya maida adadin masu anfani dakanfanin zuwa miliyan 30,891,518, sabanin na baya miliyan 30,460,528.
Kididdigar ta bayyana cewa, kanfanin Globacom ya rasa masu anfani da shi adadin mutum dubu dari 114,268, inda ya rage adadin masu anfani da layin daga miliyan 27,600,539 zuwa miliyan 27,486,271.
Kanfanin 9mobile kuwa, kididdigar ta bayyana cewa ya samu karayar masu anfani na adadin mutum dubu 74,031, inda ya rage jimillar masu anfani da su daga miliyan 9,808,935, sabanin na watan Janairu da su ke da miliyan 9,882,966.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!