Connect with us

KASASHEN WAJE

Al-Sisi Ya Gana Da Haftar Na Libiya An Sabon Rikicin Tripoli

Published

on

Shugaban Kasar Masar Abdel Fattah al-Sisi ya gana da Khalifa Haftar na Libiya a birnin alkahira, dai-dai lokacin da Haftar ke ci gaba da fuskantar matsin lamba daga Kasashen duniya kan hare-haren da ya ke kai wa Tripoli da nufin kwace birnin.
Shugaba Al-Sisi dai na matsayin aminin Khalifa Haftar, wanda ke rike da ikon gabashin kasar kafin karbe ragama da kudanci gabanin fara yunkurin kwace iko da Tripoli a kwanaki 10 da suka gabata. Mai magana da yawun Shugaba al-Sisi ya ce Shugaban ya gana da Haftar ne game da halin da ake ciki yanzu haka a Libya, dai-dai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ke cewa rikicin ya hallaka mutane 120 tare da jikkata 600.
Kawo yanzu dai babu cikakkun bayanai daga bangarorin biyu yadda tattaunawar ta gudana ko kuma matakan da za a dauka dai-dai lokacin da rikicin na Libya ke kara tsananta, sai dai fadar Gwamnatin Masar ta fitar da wani hoto da ke nuna al-Sisi tare da Haftar a gefe kuma ga Shugaban sashen Fikira na Libya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!