Connect with us

RIGAR 'YANCI

Alhaji Musa Shehu Yaro Ya Zama Mardannin Gabas Na Zazzau

Published

on

A ranar juma’ar da ta gabata Mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, ya nada Alhaji Musa Shehu Yaro matsayin Mardannin Gabas na Zazzau, wanda taron nadin ya gudana a fadar Zazzau.
A jawabinsa jim kadan bayan kammala nadin , mai martaba sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris ya bukaci Alhaji Shehu Yaro, day a ci gaba da halayensa na tallafa wa al’umma musamman , yadda ya ke tallafa wa matasa wajwn ci gaba da karatu da kuma duk wani batu da ya shafi sana’o’in dogara kai da kuma zaman lafiya a masarautar Zazzau ba ma jihar Kaduna baki daya.
Alhaji Shehu Idris ya kuma yi kiura ga sabon Mardannin Gabas na Zazzau, day a ci gaba da aiwatar da tsare–tsaren da za su zaman kara samun zaman lafiya a masarautar Zazza da kuma kasa baki daya.
Sabon Mardannin Gabas na Zazzau A lhaji Musa Shehu Yaro, an haife shi ne a birnin Zariya a shekara ta 1964, bayan ya yi nisa karatun Allo a makarantar azure sai kuma aka sa shi a makarantar firamare da ke Tudun Wada Kaduna,bayan ya sami takardar kammala wannan karatu, sai ya sami shiga kwalejin Rimi [RIMI COLLEGE ] da ke garin Kaduna, inda ya kammala wannan kwalejin a shekara ta 1982.
Bayan kammala makarantar sakandaren da aka ambata da kyakkyawar sakamakon jarabawa, sai ya sami shiga kwalejin share fagen shiga jami’a [ CAST ] da ke Zariya, , a nan ma bayan ya sami kammalawa salun-alun, sai ya sami shiga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda ya yi karatu domin neman digirn farko a fannin harkar kasuwanci, ya kuma kammala a shekara ta 1987.
Har ila yau, ya sake komawa wannan jami’a ta Ahmadu Bello, inda ya sami digirinsa na biyu, kan harkar bunkasa kasuwak, a shekara ta 1994,sai kuma a shekara ta 2003 wata babbar difiloma kan yadda ake tsara harkokin sufuri, inda ya sami wannan difilomar a cibiyar kimiyyar sufuri, ta Nijeriya [ NITT ] da cibiyar ta ke Zariya.
Alhaji Musa Yaro, ya fara aikin gwamnatin jihar Kaduna a hukumar kula da tattara kudaden shiga ta jihar Kaduna, a matsayin mai tattara kudaden shiga mai daraja ta daya a shekara ta 1988, wanda da tafiya–ta yi– tafiya sai da ya kai matsayin babban jami’in tara kudadaen shiga a jihar Kaduna a shekara ta 1994.
Daga aikin da ya ke a gwamnatin jihar Kaduna, Alhaji Musa Shehu Yaro, ya koma aiki a hukumar kula da sufurn ruwa Nijeriya [ NPA ] inda ya fara da mataimakin manaja, saboda kwazon day a ke nuna wa a wurare da bangarorin a wannan hukuma ta [ NPA ], sai da ya kai matsayin mataimajin manaja a wannan hukuma.
Alhaji Musa Shehu Yaro, ya na cikin kungiyar akantoci ta Nijeriya, da kungiyar masana harkokin saye da kuma sayarwa [ CIPSM ] da kungiyar da suke da bayar da labrin kudade ta Nijeriya []FRCN [] da dai kungiyoyi ma su yawan gaske da suke ciki da wajen Nijeriya.
A zantawar da wakilinmu ya hyi da Sabon Mardannin Gabas na Zazzau, bayan ya karbi mubayi’a daga ‘yan uwa da abokan arziki da suka kasance a fadar Zazzau, domin shaida wannan nadi da mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris ya yi ma sa, da farko ya nuna matukar jin dadinsa da wannan nadi da mai martyaba Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris ya yi ma san a Mardannin Gabas Na Zazzau.
Ya cigaba da cewar,babu tantama, ya dauki wannan nadin da mai martaba Sarkin Zazzau ya yi ma sa a matsayin kaimin da zai kara tashi tsaye domin aiwatar da ayyukan da za su tallafa wa al’umma, da kuma hada hannu da dukkan wanda ked a kudurin ciyar da masarautar Zazzau da jihar Kaduna da kuma Nijeriya gaba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!