Connect with us

Uncategorized

An Bukaci A Karfafa Ilimi Da Siyasar Matan Arewa

Published

on

An bayyana cewa mata a Arewacin kasar nan sun kai matsayin da duk inda ka duba a harkokin manyan ayyuka da mu’amalar kasuwanci su na taka muhimmiyar rawa a fannoni daban-daban da su ka hada da likitanci, injiniyoyi, bangaren shari’a, ciniki da kasuwanci da harkokin siyasa, amma duk da haka akwai bukatar a samu karin cigaba sosai ya shafi dukkan mata na birni da na karkara.
Daya daga cikin mambobi na mata masu kishin jihar Kano, Maryam Hamza Umar ta bayyana haka da take zantawa da manema labarai jin kamma taron da su ka gudanar.
Ta ce burinsu Mata a kowane mataki su sami ilimi da wayewa, yanzu a fannin ilimi Mata har ana samun Shehinan Malaiman jami’oi a cikinsu da sauran bangarori na kwarewa a ilimi, duk da haka suna da bukatar ilimin da ake samu a tsakanin mata ya zama suna anfani da shi yadda ya kamata a Arewa. Ta yadda za a sami yawaitar mata a siyasa, kasuwanci da ciniki da duk wani fanni na ci gaban zamani da bai sabawa ka’ida ta addini da al’ada ba.
Maryam Hamza Umar ta yi nuni da cewa idan aka ilmantar da Mace guda daya daidai yake da ilmantar da al’umma saboda matsayin da suke takawa na ci gaban al’umma. Mata na taka rawa a siyasa a Arewa, amma ba yanda ba saboda suna so su fito amma yanda aka dauke su a cikinta ita tasa mata ke dari-dari, domin duk wacce take siyasa a kasar hausa ana daukarata mai budewar ido mara kamun-kai. A baya ma duk wacce take siyasa takan rufe idonta ne, har kyamarta ake saboda yar siyasa ce.
Ta kara da cewa shi yasa ma wadanda basu da ilimin zamani suka fi shiga a dama dasu, a fita yakin neman zabe dasu, shugabannin Mata su fito ayi yawon siyasa dasu, amma idan aka zo bada mukami in an kafa gwamnati ba’a basu, sai a nemo wata wanda wani nata keda alaka da jagororin siyasar ayi mata mukami, saboda wadanda aka yi dawainiyar siyasar da su matan ba su da ilimi da za a ba su mukami.
Ta ce, amma yanzu so suke mata su fito su fito siyasa a basu gurbi da za su kawowa yan’uwansu Mata ci gaba don sune suka fi taka rawa a zabe, muga idan an tashi basu tallafi na siyasa na kawowa mata ci gaba, ba’a dauko dauko wadanda basu wahala ba yin hakan shi yasa baya anfanar mata, amma idan aka da wadanda suka san abin suka wahalta za su fi anfanarwa.
Maryam Hamza ta ja hankalin masu harkokin siyasa Mata su rika neman Ilimin zamani dana addini hakan zai taimakawa bunkasa siyasar Mata. Ta bada misali da cewa ita kanta tana harkar siyasa tsawon lokaci da yawa tana tallafawa mutane, amma gudun karsu nuna kansu sosai a daukesu marasa kima, domin duk wanda yazo neman aurenka sai ace ai harkar siyasa take me zaka yi da ita? Idan za a cire wannan irin kyamar da ake nunawa mace a harkar siyasa kowa zai fito ya yi siyasa baisa ka’ida ta shari’a ba tare da wuce gona da iri ba.
Ta ce, rashin bai wa mata dama ta sana’a na da tasiri wajen tauye rayuwarsu ya kamata idan mace ta ce, za ta yi wani abu n a barta tayi kar a takura mata illa a rika lura da ita karta wuce matsayinta kuma a rika karfafa mata gwiwa wajen yi kaza gyara kaza hakan zai taimakawa ya kyautatawa ci gaban rayuwar iyalai. Ta ce, a matsayinta ta mace data tashi tun tanada shekaru Uku mahaifinta ya rasu,mahaifiyartace ta bata kulawa ta yi karatunta na Firamare dana sakandire a Kano da Jigawa har tayi digiri a jami’ar Bayero take aikin a halin da ake ciki yanzu bisa irin tarbiyyar data samu, don haka idan aka bai wa Mata tarbiyya ta ilimin addini dana zamani duk abinda mace za ta yi za ta kare mutuncinta. A tarihin kasar hausa kowane Gida da irin sana’ar da suke tashi da ita banda kasuwanci da noma da ake zaka samu wasu musamman mata na daddawa, kuli-kuli, kosai, saka, dinkin hula, wanda bai kamata ace ana barin wannan sana’a ba, mata da maza dan sun yi boko bai kamata ace sun bar sana’ar gado ba a kawo mata ci gaba na zamani yanda idan kayi abinka za’a iya dauka akai wasu wurare a sayar. Irin sana’oi da mata suke a gida a duba aga yanda za a ci gaba da ingantasu su girmama da aduk duniya za a tallatasu idan an samu ci gaba ribarce.
Maryam Hamza Umar ta yi kira ga Gwamnatocin Arewa su rika taimakawa Mata na gida masu sana’oi domin su tsaya da kafafunsu ta basu horo mai inganci da jari mai kauri dazai wadacesu suma harsu dauki wasu ma’aikatan a karkashinsu hakan zai taimaka wajen rage talauci da rashin aikin yi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!