Connect with us

LABARAI

An Maka NSCDC A Kotu Bisa Mutuwar Wanda Su Ka Tsare

Published

on

Wani Lauya, Morakinyo Ogele ya sa karar hukumar tsaro ta NSCDC (Cibil Defence) a Kotu bisa mutuwar wani da ke tsare, Razak Ahmed a ofishin hukumar a jihar Ondo.
Shi dai Ahmad din , jami’an hukumar sun kama shi ne a watan Maris da ya gabata bisa zargin yin lalata da diyarsa mai shekaru 8 da haihuwa.
Rahotanni sun bayyana cewa, ya mutu a ofishin jami’an tsaron da ke babban birnin jihar ta Ondo, Akure kwanaki uku bayan kama shi.
Iyalan mamacin dai, sun zargi jami’an da azabatar da shi domin tilas ta shi karba laifin da ake tuhumarsa da shi, abin da ya yi sanadiyar mutuwar shi, kamar yanda iyalan ke zargi.
To sai dai, mai magana da yawun hukumar, Samuel Oladapo, ya musanta zargin, inda ya ce, Ahamad din ya kashe kanshi ne a inda ake tsare da shi, ba kamar yanda ake zargi ba.
A dalilin rashin gamsuwa da bayanin, Lauya Samuel Oladapo ne ya garzaya babbar Kotun tarayya mai mazauni a Akure, inda ya saka karar hukumar a madadin iyalin mamacin, yana mai neman adalci kan lamarin.
Lauyan yana neman Kotun da ta ba wa hukumar umurnin bincikar jami’anta da ke da hannu da kama shi, tsare sa, da kuma zargin azabtarwa zuwa mutuwa da ake yi a kan ma’aikatani.
Haka kuma, har wa yau, yana neman Kotun da ta ba hukumar umurnin mika jami’an da ake zargi da hannu wurin mutuwarsa zuwa ga hukumar ‘yan sanda domin gudanar da sahihin bincike, da kuma hukunta su.
Ba iya nan ya tsaya ba, Lauyan ya nemi Kotun da ta umurci hukumar jami’an tsaron ta ‘Cibil Defence’ da ta biya iyalin mamacin kudi naira miliyan 500 na bata ma dan uwansu suna da su ka yi.
Lauyan kuma, ya roki kotun da ta umurci hukumar da ta tura dukkanin jami’anta zuwa gwajin kwakwalwa domin hana afkuwar azabtarwa zuwa mutuwa nan gaba, da kuma samun shaidar lafiyarsu dan tabbatar da cewa basu da matsalar kwakwalwa.
A cikin takardar koken mai dauke da shafi 33 da Lauyan ya mikawa Kotun, ya bayyana cewa, ya dauki matakin saka karar ne domin ‘yan uwan mamacin, da kuma al’umma gabakidaya.
Lauya Samuel ya bayyana cewa, “Yan uwan mamacin sun yi ta kiraye-kiraye ga kungiyoyin kare hakkin bil’adama na su taimake su kan ganin cewa sun samu adalci kan lamarin.”
“Ba dan komai ba sai dan ganin yanda hukumar NSCDC ke kokarin rufe wannnan mummunan kisan kan. Sam basu damu da mummunan abin da suka aikata wa iyalan mamacin ba.”
Ya ci gaba da cewa, “ Mai magana da yawun hukumar ya ce mamacin ya kashe kansa ne a inda yake tsare. Ni kuma nake cewa, ina ganin, an samar da hukumar NSCDC ne domin kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Nijeriya. Ba aikin jami’an hukumar ba ne kisan kai.”
Yan uwan mamacin sun zargi cewa, jami’an sun yi ta dukan sa ne da sanda har ya zama ya mutu a inda suke tsaren da shi.
A nasu bangaren kuwa, hukumar jami’an tsaron ta musanta hakan, inda mai magana da yawun hukumar ya bayyana cewa, mamacin ya kashe kansa ne ta hnayar sargafe kans da ya yi a cikin dakin da yake shi kadai.
A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ta hannun kakakinta, Mista Oladipo, sun bayyana cewa, “Ma’aikatanmu na unguwa ne suka kamo shi, inda suka mika shi babban hedikwatarmu domin gudanar dabincike. A lokacin da muke bincikarsa, wanda ake zargin, ya karba laifin da ake zarginsa da shi, inda ya ce, sharrin shaidan ne ya sashi aikata hakan.”
“Kafin mu kai shi a dakin ajiya a cikin ofishin namu, ya yi ta kokawa da cewa yana jin sanyi, inda ya roke mu da mu bar shi ya saka babbar rigarsa, muka lamunce mai hakan.”
Ya ci gaba da cewa, “To bayan haka, sai muka kawo shi a hedikwatarmu da misalin karfe 6 na yamma, abin mamaki, lokacin da wani ma’aikacinmu ya je dakin da ake tsare da shi don kaima sa abincin da ‘yan uwansa suka kawo masa, sai muka sami ya rataye kansa a wata kofar karfe da ke jiki.
“Abin takaici, kasancewar sa a cikin dakin da ake tsare da shi, shi ne abin da ya bashi damar aikata wannna mummunan abun,” inji shi a cikin sanarwar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!