Connect with us

KASUWANCI

Babu Karancin Man Fetur Da Zai Faru A Nijeriya – PPRA

Published

on

Hukumar dake sanya ido akan farashin mai da dangogin sa PPRA ta shawarci yan Nujeriya akan kada suji wani tsaoro cewar za’a samu karancin man fetur a Nijeriya.
Babban Sakataren Hukumar ta PPRA Malam Abdulkadir Saidu ne ya sanar da hakan a cikin sanarwar da ya fitar, inda ya jadda da cewar, Nijeriya tanada wadataccen man fetur a yanzu da zai wadaci kasar.
Malam Abdulkadir Saidu ya baiwa yan Nijeriya tabbacin cewar, su manta da sayen man fetur din don tara shi a bisa tunanin za’a samu karancin sa domin Nijeriya tanada wadataccen man fetur a yanzu din da zai wafaci bukatun yan Nijeriya.
Acewar sa, a bisa nauyin da aka dorawa Hukumar ta PPPRA wajen sanya ido akan samar da man da kuma rabar dashi Hukumar ta tanadi rumbun adana bayanai da kuma sanya ido akan yadda ake rabar da man kamar yadda doka ta tanada.
Malam Abdulkadir ya kuma sanar da cewar, yawan PMS da ake rabarwa a kullum a shekarar 2017 zuwa shekarar 2018 da kuma shekarar 2019, ta kai kimanin miliyan 46 da kimanin miliyan 54 da kuma kimanin miliyan 56 na liticin man, inda ya yi nuni da cewar, hakan ya nuna cewar an kara samun karuwar yadda rabar da man a shekarar 2019.
Ya sanar da cewar, a bisa bayanan da ake dasu, an rabar da isasshen PMS wanda zai kai samada kwanuka 21 a zaman wadatacce.
A karshe Malam Abdulkadir ya shawarci masu yin amfani da man fetur a Nijeriya kada su firgita wajen sayen man don tara shi kuma Hukumar, zataci gaba wajen sanaya ido akan yadda ake rabar da man don tabbatar da ba’a samu wata tangarda ba wajen rabar da man a daukacin fadin kasar nan.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!