Connect with us

MAKALAR YAU

Dumama Da Canjin Yanayi

Published

on

A watan Disambar bara aka samu ruwan sama a wasu daga jihohin Arewa, ciki har da Abuja, sabanin yadda aka saba samun bisa tsarin jadawalin ilimin Jugrafi da yake nazartar halayyar kasa. A watan Maris din da ya gabata kuwa aka samu jerin kusan mako guda ana wani irin mai hade da yanayin sanyi tare da zafi-zafi kadan tun daga Abuja har zuwa jihar Kano. Abin ya zo wa kowa da mamaki banda iri na yan kadan da dama mun sha fadar hakan za ta iya faruwa.
Lokacin da akai ruwa a watan Disamba, dayawa wasu sun dauka saukar rahama ce, amma ni ina kallon hakan a matsayin wata manuniya da Allah yake so ya nunamana cewa mu shirya ko kuma azabarsa ta isa garemu baki daya! Kuma dai kun san idan azaba tazo bata barin wai wanda zai ce babu ruwansa. Idan ta tashi zuwa to kan mai-uwa-da-wabi take dira. Idan iri na basu yi magana ba to tabbas wata rana dukanmu tare za mu yi gudan hijira ko kuma mu dinga rububin karbar tallafi daga kasashen waje. Wa zai so haka? Allah ya kiyaye. Wannan ruwan da aka samu na nuni da gurbacewar yanayi ne. Mun sassare bishiyoyinmu kuma mun kasa dasa wasu. Zai yi wuya ka ga yanzu, a unguwannin da ba tsarin gwamnati ba, an yi bishiyoyi a kananun gidajen da muke zaune aciki. A wata sabuwar unguwa ko a Kano da aka dauko hotonta daga tagar jirgi, an gano babu alamun kore sai dai ja kawai. Wata alama da take nuni da cewa mun sare bishiyunmu kuma mun kasa dasa wasu.
To amma fa Allah ba ya kiyayewa sai mun kiyaye da kanmu. Allah ba ya canjawa mutane komai sai abinda suka fara canjawa da kansu. Lokacin da Allah yace ya sanar da Annabi Adamu sunaye ba wai yana nufin cewa kai ma ka zauna kana rokon Allah ya sanar da kai sunaye bane ba tare da ka yi yunkuri da kanka ba. Allah ya fada cewa shi fa da Alkalami yake sanarwa. Domin ka nemi Allah ya sanar da kai to sai ka dauki kayan karatu, littafi da Alkalami, domin ka cigaba da nazari don ya sanar da kai ilimi. Ta haka Allah yake sanar sa mutum abinda bai sani ba. Da wannan siyakin za mu gane cewa akan komai da zaka roki Allah to kana bukatar ka yi wani kokari a matakin farko domin sai ka tashi Allah zai taimakeka. Babu dalilin zama a gida kuma kana cewa Allah ya kaika China ko Amerika kuma kana kwance. Sai ka nufi filin jirgi to kuma sai ka yi addu’ar Allah ya kiyaye hanya kuma ya kaika lafiya domin shi yake da iko da jirgin da kuma mai tukin jirgin. Wannan na fara bayani akai ne don kada wani ya dauka cewa Allah yana abu babu sababi ne.
Duk lokacin da aka kaucewa tsarin Allah akan komai to za’a hadu da matsaloli. Mutane suna dauka zunubi ne yake janyo gurbacewar muhalli ko saukar azaba. Babban zunubin da yake janyo lalacewa da gurbacewar muhalli shi ne kaucewa tsarin da dabi’a take dashi. Duk wanda ya gurbata ruwan sha to zai samu annobar cutar kwalara. Wanda ya tashi bom din nukiliya to tabbas zai ruguza gari ne. Duk abinda yake samun mutane na azabar da take fita da musiba to mutanene da kansu suka janyo. Lokacin da mutane suka yanke bishiyu kuma suka fitar da iskar gas mara kyau to tabbas suna rusa muhallinsu da hannunsu ne. Kada musibar tazo kuma mutane su ce Allah ne ya jarrabesu bayan su suka tsoma hannunsu dakansu!
Wannan ruwan da aka gani a watan Disamba da kuma hazon da aka gani a watan Maris, alama ce ta cewa akwai barazanar canjin yanayi saboda dumamar yanayi. Yan bishiyun da suke sanyaya muhallin duk an ciresu. An fi bukatar fili ko gawayi fiye da yadda rashin bishiyu suke barazana ga muhallinmu. Bara na gayamaka illar da hakan za ta iya janyowa. Ka dauka kai manomi ne da ka gama hada shukarka kana jiran ruwa a watan Yuni. Maimakon kaga ruwan sama a watan sai kawai ka ga sanyi ya buso shukarka duk ta bushe! Idan fa ba kai kadaine kayi shukarba to duka manoma wannan canjin yanayi zai shafa. Daga nan sai fari saboda canjin yanayi. Wannan shi ne karamin misali da zan iya baka na matsalar da canjin yanayi za ta iya bayarwa.
Me ya kamata mu yi tun kafin wannan matsalar ta yi karfi? Tun yanzu ya kamata mu yi babban shiri wajen wayar dakan al’ummarmu muhimmancin dasa bishiyu a matakin farko da kuma illar sare bishiyu. Gwamnati na nata kokari wajen ganin an dena amfani da injina masu fitar da hayakin da za su iya lalata sararin sama, saura ga kungiyoyi masu zaman kansu da su dinga bita ta musamman don ilimantar da al’umma kan muhimmanci gyaran muhalli da kuma dasa bishiyu a inda ya dace. Mu dena sare bishiyu ba tare da dasa wasu ba domin hakan babbar illa ce ga rayuwarmu. Malamai ma za su iya taka rawarsu anan. Ni tunda nake karatu ban ga wani addini da ya kai na Musulinci mutunta bishiyu ba. Hatta lokacin yaki an haramtawa musulmi ya sare bishiya ko da a garin da ba nasa bane. Hadisai masu yawa sun bayyana cewa dasa bishiya hade yake da babban lada mai yawa don ana lissafa ladan gwargwadon ‘ya’yan bishiyar ne.
Dukkaninmu muna da hanyoyin da zamu taimaki duniyarmu. Kuma dai taimakon duniya tamkar taimakon bayin Allah ne. Shi kam Allah bai da babban abinda yake so mu yi fiye da mu taimakawa bayinsa. Lokacin da yace a rantamasa bashi ma ai bayinsa yace a bawa. Lokacin da ya kira masallaci dakinsa ai bayinsa ne suke shiga. Masallaci kuwa ba iya gurin sallah bane; makaranta ce hade da gurin zaman bayin Allah. To idan muka taimaki duniya ta hanyar kubutar da ita daga dumamar yanayi to kamar mun taimaki bayin Allah ne wadanda za su iya salwantar da dukiyarsu da kuma rayuwarsu saboda gurbacewar yanayi. Kowannenmu zai iya dasa bishiya ko a gurin aiki, ko a makaranta ko kuma a wani dajin. Bishiya guda daya da zaka dasa za ta taimaki duniya. Hausawa ma na cewa : wanda za shi sama ya taka leda ai ya rage hanya. Ina ga wanda zai taimaki duniya kuma ya dasa bishiya ko da guda daya ce?
Ya kamata kuma gwamnati ta dawo da al’adar dasa bishiyu acikin ma’aikatunta da kuma makarantunta. Kai har makarantun da ba na gwamnati ba a sanya su bisa tsarin dasa bishiya. Na je firamaren da na yi na ga duk an sare bishiyun da na sani akwai a lokacin ina dalibin makarantar. Akwai wata firamaren kusa da gidanmu ita ma dai yanzu duk babu bishiyoyin dogon yaro da na sani a makarantar tun ina yaro. A makarantar da na koyar kuwa, wata karamar sakandare ta mata, babu ko da bishiya guda daya balle kuma ciyawa. To idan aka rasa bishiyu a guraren gwamnati a ina kuma za’a samu?
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!