Connect with us

RIGAR 'YANCI

El-Rufai Ya Nada Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnati A Matsayin Kwamishinan Kudi

Published

on

Gwanatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin Malam Nasiru Ahmed El-Rufa’i, ta bayyana sunan Mohammed Bashir Sa’idu, a matsayin sabon kwamishinan ma’aikatar kudi ta Jihar kaduna, bayan tsohon kwamishinan Suleman Abdu Kwari , ya lashe zaben Dan majalisar dattawa mai wakiltar Arewacin Kaduna a majalisar Dattawa ta Nijeriya a zaben da ya gabata.
A wata sanarwar da gwamnatin ta fitar Wanda mai baiwa gwamnan shawara akan harkokin yada labarai, Mista Samuel Aruwan ya sanyawa hannu, ya ce, Bashir Sa’idu shi ne ya maye gurbin tsohon kwamishinan Wanda yanzu zabebben Dan majalisar Dattawa ne.
azalika, sanarwa tace babban sakataran ma’aikatar kudi ta jihar Mista Nyam, shi ne sabon Akanta janar na jihar.
Bashir Sa’idu Wanda tsohon kwamishinan ma’aikatar kananan hukumomin jihar ne daga shekarar 2015 zuwa 2016, Wanda kuma shi ne ke rike da mukamin shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar Kaduna ,har ya zuwa yau da aka Nada shi kwamishinan kudin jihar
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!