Connect with us

KASUWANCI

Hukumar Sayar Da Hannun Jari Ta Bukaci Yin Hadaka Da Masu Kula Da Hada-Hadar Kudi

Published

on

Hukumar sayar da hannun jari ta kasa SEC ta ayyana aniyar ta na karfafa yin hadaka da sauran masu kula da hada-hadar kudi don yin gangamin wayar da kai akan hada-hadar kudi.
Hukumar ta bayyana cewar, a bisa kokarin da take yi don tabbatar da an wayar da kan yan Nijeriya da suke a yankunan daukacin birane da kuma karkara akan alfanun dake tattare shiga yin hada-hadar kudi, inda kuma hakan zai kara habaka tattalin arzikin Nijeriya.
Daraktan Hukumar na sashen ciyar da kasuwanci ga Mista Edward Okolo ne ya bayyana hakan a lokacin da suka kaiwa kwamitin kudi na wayar gangamin wayar da kai na Hukumar Insora ta kasa NAICOM a birnin tarayyar m Abuja a ranar Lahadin data gabata.
Bayanin nasa wanda yake kunshe a cikin sanarwar da Hukumar ta SEC ta fitar Mista Okolo ya sanar da cewar, a bisa kokarin da akeyi na tabbatar da karfafa hadakar a tsakanin kwamtin da kuma Hukumar ta NAICOM ya kuma bayyana godiyar sa ga Hukumar ta NAICOM akan kasancewar wakiliya a cikin kwamitin musamman wajen taimakawa don wayar da kan a kasuwar.
Ya danganta Hukumar ta NAICOM a matsayin daya daga Hukumomin da suke tara kudi daga kasuwar, inda ya yi nuni da cewar, akwai bukatar a samar da dama don fadakarwa akan inshora a lokacin gangamin wayar da kan a kasuwar.
Shima a nasa jawabin, daya daga cikin wakilan kwamitin Mista Omagbitse Barrow ya bayyana cewar, a irin halin da fannin kudin yake a yanzu, akwai bukatar ayiwa hukumomin da abin ya shafa garanbawul.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!