Connect with us

RAHOTANNI

Iyayen ’Yan Matan Makarantar Chibok Sun Roki Boko Haram

Published

on

Bayan bikin cika shekaru biyar da sace yara mata ‘yan makarantar Sakandare ta Chibok, da ‘yan ta’addan Boko Haram suka yi, iyayen yaran sun yi kira ga ‘yan ta’addan na Boko Haram da su sako sauran ‘ya’yan na su da suka saura a hannun su.
Wasu daga cikin iyayen yaran sun shaidawa wakilinmu a Maiduguri, ranar Lahadin nan halin kuncin da suka shiga a kan sace ‘ya’yan na su da ‘yan ta’addan na Boko Haram suka yi a makarantar Sakandare ta garin na Chibok a ranar 14 ga watan Afrilu, 2014.
Taron tunawan wanda wata kungiya wacce ba ta gwamnati ba ce mai suna, ‘Al’amin Foundation for Peace and Development’ ta shirya shi. Akalla yaran makaranta mata 270 ne aka sace, wasu daga cikin ‘yan matan sun sami tserewa, da suka hada da Amina Ali.
Sannan wasu kuma su 21 sun sami kansu a watan Oktoba, 2016, sa’ilin kuma da Sojoji suka ceto yarinya guda a watan Nuwamba, na wannan shekarar.
Hakanan, wasu ‘yan matan 82 sun sami kansu a sakamakon tattaunawar da aka yi da gwamnati a watan Mayu, 2017, inda kuma yarinya guda ta sami tsira a watan Janairu, 2018.
Recheal Daniel, uwa ce ga daya daga cikin yan matan da aka sace mai suna, Rose Daniel, ta yi kira ga shugaban daya bangaren na ‘yan ta’addan na Boko Haram, Abubakar Shekau, da ya hakura ya sako mata diyarta.
Recheal Daniel, ta koka da cewa lamarin ya sabbaba mata ciwuka iri-iri da bakin ciki, ta kara da cewa, mijinta shi ma ‘yan ta’addan sun kashe shi.
Ta ce, tun daga wancan lokacin, ita kadai take daukan nauyin sauran ‘ya’yan na shi shida da mijin nata ya tafi ya bari.
Ayuba Alamson, wanda shi ke rike da wasu daga cikin ‘yan matan da aka sace, ya ce, yaran hannun na shi shida ne aka sace a makarantar ta Chibok a wannan ranar.
Ayuba Alamson ya ce, an sako uku daga cikin yaran na shi, yayin da sauran har yanzun ba a sako su ba.
Ya koka da cewa, kimanin 18 daga cikin iyayen ‘yan matan da aka sace sun mutu a sanadiyyar halin damuwan da suka shiga a kan sace ‘ya’yan na su.
Ayuba Alamson, ya bukaci gwamnatin tarayya, Majalisar [inkin Duniya, da Kungiyoyin Duniya da kar su gaza a kokarin da suke yi na ganin an sako ‘ya’yan na su.
“Ina kuma rokon da a sako, Leah Sharibu, yarinya guda da ta saura a hannun ‘yan ta’addan na Boko Haram, bayan da suka sako sauran ‘yan matan 112 da suka sata daga makarantar Sakandare ta garin Dapchi, Jihar Yobe.
Shi ma wani mazaunin garin na Chibok, Musa Maina, ya yi roko ne da a sako ma shi matarsa, Zahra Musa, da diyarsa, Hadiza Musa, da ‘yan ta’addan suke rike da su.
Maina ya yi tilawar yanda ya sami tserewa daga garin na Chibok, zuwa Konduga, a ranar 14 ga watan Afrilu, inda ya fada cikin wani tarkon na ‘yan ta’addan.
“Mutane biyu ne suka zo gidana da bindigogi suna neman su kashe ni. Ni da matata ta biyu mun sami damar guduwa, amma sun tafi da Uwargidana da diyarta,” in ji shi.
A nata bangaren, Hamsatu Allamin, daraktan kungiyar ta, Al’amin Foundation for Peace and Debelopment, cewa ta yi, dubannan mata da yara ne ‘yan ta’addan suke garkuwa da su.
Ta bayyana cewa kungiyar na su ta shiga wayar da kai sosai a kan yawan mata da yaran da ‘yan ta’addan suka sace a yankin na arewa maso gabas.
Ta yi kira da a dauki kwararan matakai na ganin an ceto yara mata ‘yan makarantar na Chibok, da sauran mutanan da ‘yan ta’addan suke yin garkuwa da su a duk sassan kasar nan.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!