Connect with us

WASANNI

Kofin Africa: Mu Na Bukatar Addu’ar ’Yan Najeriya – Manu Garba

Published

on

Tawagar kwallon kafar Najeriya ta matasa ‘yan kasa da shekara 17 ta yi nasara a kan mai masaukin baki Tanzaniya da ci 5-4 a karawar da suka yi ranar Lahadi kuma wannan shi ne wasan farko da aka bude gasar ta matasa ‘yan 17, domin fitar da wadanda za su wakilci Afirka a gasar kofin duniya.
Bayan da Najeria ta hada maki uku a rukunin farko, idan anjima ne Angola da Uganda za su kece raini a daya karawar rukunin farko sannan a yau rukuni na biyu zai fara wasa tsakanin Morocco da Senegal daga baya a kece-raini tsakanin Guinea da Kamaru.
Tawagar Najeriya wadda Manu Garba ke horas da ita, za ta yi wasa na biyu a gobe Laraba da Angola ita kuwa mai masaukin baki Tanzaniya wadda ta yi rashin nasara a wasan farko za ta yi wasa na biyu da Uganda a dai gobe Laraba.
“Mu na bukatar samun nasara a wasa na gaba domin a wasannin rukini idan kasami nasara a wasanni biyu tabbas zaka samu kwarin guiwar zuwa mataki na gaba kuma muna fatan zamu samu damar yin hakan” in ji kociyan tawagar, Manu Garba
Ya cigaba da cewa Yan wasansa sun shirya tsaf domin bugawa da kowacce kungiya kuma ya gayawa ‘yan wasan cewa a gaba daya gasar babu wata tawagar mai sauki saboda haka suci gaba da dagewa.
A karshe kuma yayi kira ga ‘yan Najeriya dasu cigaba da yiwa ‘yan wasan addu’a domin ganin sun samu nasara a gasar sannan kuma suje su wakilci nahiyar Africa a gasar da za’a buga ta duniya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!