Connect with us

LABARAI

Kungiyar Kimanta Kadarori Ta Jihar Kano Ta Dukufa Wajen Fadakar Da Al’umma

Published

on

Kungiyar kididdiga da kimanta kaddarori ta jihar Kano, Estate Surbeyors and Balurs ta dukufa wajen wayar da kan daliban jihar Kano game da muhimmancin kwas din a a makarantun dake fadin jihar Kano.
Wannan bayani a fito ne daga bakin mataimakin kungiyar ta jihar Kano, Abdurrauf Umar Nadabo rsb, a lokacin da yake zantawa da manema labarai kwanakin baya a Kano. Mataimakin shugaban kungiyar ya ci gaba da cewa domin ganin kwas din ya samu karbuwa a fadin jihar ya sa suke kai ziyara wasu daga cikin makarantun sakandare inda suke wayar wa da dalibai kai, musamman irin darussa da kuma makarantun da za su shiga bayan sun kammala karatun su na sakandare.
Malam Abdurrauf Umar NaDabo rsb, ya ce shekarun baya ba ‘a karantar da wannan fanni a wasu daga cikin kwalejojin ko jami’oin da ke arewacin kasar nan, yawanci an fi karantar da shi ne manyan makarantun dake kudancin kasar nan wannan ya sa daliban dake karatun shi suka yi karanci a yankunan Arewa.
Amma in ji mataimakin shugaban yanzu an samu canjin da a ke karantar da kwas din a wasu jami’oin kasar nan kamar ATBU Bauchi, UNI Jos, Kaduna Poly, Ramat Poly dake Maiduguri da kuma Kauran Namoda. Jami’ar BUK da ke Kano ita ma ana karantar da wannan fanni da kuma wasu makarantun dakwe jihar.
Domin ganin fannnin ya samu gindin zama a BUK kungiyar su ta sayi littafai masu tarin yawa akan fannin , haka kuma kungiayr su na daga cikin wadanda suka tsaya tsayin daka wajen ganin a na karantar da faninin a jami’ar ta BUK.
Abdurrauf Umar Nadabo RSB, ya ce duk karshen wata kungiyar su na gudanar da taro har da wadanda ba su riga sun mallaki lasisi ba da inda ake tattauna yadda za ‘a ciyar da kungiyar gaba da kuma magance matsalolin da ke a ke da su.
Amma babbar matsalar da ke addabar kungiyar a jihar Kano ita ce har yanzu akwai karancin mutane da ba su fahimci muhimmancin kwas din ba, sai ya yi kira ga al’ummar arewacin kasar nan musamman dalibai da su shigo, domin neman ilimin fannin a manya da kananan makarantun da ke yankin na Arewa ya ce, idan har mutum ya samu nasara ko kuma kwarewa a kan ilimin Estate Surbeyors and Baluers, idan mutum bai samu aiki a gwamnati ba zai iya samu a banki ko wasu daga cikin manyan kamfanoni dake kasar nan ko kuma ya zama yana aiki mai zaman kanshi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!