Connect with us

Uncategorized

Kwalara Ta Kashe ’Yan Gudun Hijira 175 A Sansaninsu, In Ji MDD

Published

on

Hukumar kula da harkokin kiwon lafiya ta duniya da ke karkashin Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana asarar rayukan da a ke samu a sansanin ’yan gudun hijira sakamakon cututuka da ke addabar al’umma.
Da ya ke magana a madadin jami’in kula da harkokin kiwon Lafiya, Dakta Durkwa, ya ce, cutar Kwalara da Sankarau su na yin illa a sansanin ’yan gudun hijira, inda ko a shekarar da ta gabata an samu bullar cutar Kwalara a sansanonin ’yan gudun hijirar wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.
Ya ce, kimanin mutum 11,000 su ka kamu da cutar kwalarar a kananan hukumomi 28 da ke yankin Arewa maso Gabas, inda sama da mutum 175 su ka mutu.
Jihohin da abin ya faru da su sun hada da Baron da Yobe da Adamawa, inda a wannan karon hukumar kula da lafiya ta duniya ba ta yi jinkiri ba. Tuni ta dauki mata ma’aikatan kiwon lafiya na masamman guda 454 da su ke aiki na masamman wajen fadakar da al’ummar karkara gida gida kan abubuwan da ke kawo cutar Kwalara da Sankarau.
Ma’aikatan sun rika zagawa su na shiga gidaje su na wayar da kan al’umma wajen kiyaye cunkoso cikin daki guda, saboda hakan ya na rage shakar iska mai amfani.
Sannan sun gargadi da a daina barin gurare cikin kazanta da zuba gurbataccen ruwa da ke kawo sauro da miyagun kwari. Sannan a rika kulawa da abincin da za a ci da abubuwan cin abinci.
Wadannan ma’aikatan su na kokari sosai a yankin Arewa maso Gabas, kuma an ga tasirin ayyukan cikin al’umma.
Durkwa ya kara da cewa, ma’aikatan da a ka dauka duk cikansu mata ne saboda mata su na da damar su yi cudanya da ’yan uwansu mata da ke zaune a cikin gidajen aure sabanin maza.
Ya ce, “sakamakon wayar da kan al’umma da wannan bangaren ma’aikatan su ka yi ya rage fargabar da mu ke yi kasancewar abinda ya faru a shekarar 2018 na cutar Kwalara da ya kashe mutane da yawa, abin ya tada ma na hankali sosai.”
Durkwa ya ce, an kuma kara wayar ma su da kai wajen kai yara a na yi ma su allurar rigakafin Kwalara ko rigakafin cutar Poliyo, sannan a na ba su magungunan da za su taimaka wa rayuwarsu.
Shi ma da ya ke jawabi, babban jami’i a ma’aikatan kiwon lafiya ta kasa, Dakta Christopher Ugiboko, ya ce, matan da a ka sanya su wannan aikin bayan tabbatar da kwarewarsu wajen harkar kiwon lafiya sai da a ka kara ba su horo na masamman ta yadda za su yi mu’amala da matan cikin gida da yadda za su jure wa kowacce irin tambaya ko cin fuska.
A jihar Baron an samu mata 138 cikin 150 da a ka ba su horo na zagawa cikin karkara.
Shi ma a nasa jawabin Babban jami’in kiwon lafiya na Majalisar Dinkin Duniya, Dakta Clement Peter, ya ce, “mun yi farin ciki saboda canjin da a ka samu a wanan karon.”
Ya kara da cewa, yin amfani da wannan hanyar ya taimaka ma na wajen samar da kiwon lafiya da rage cututuka da ke addabar al’umma da ke rayuwa a sansanonin ’yan gudun hijira da ma karkara.
Ya ce, “al’umma sun rungumi wadannan shawarwari da mata da ke zagaye su ka ba su kuma sun yi amfani da shi, ya kuma taimake su. Ba mu samu damuwa kamar a shekarar da ta gabata ba.”
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!