Connect with us

ADABI

Littafin ‘Mene Ne Sanadi? Na Rabi’atu SK Mashi (9)

Published

on

Ko sati biyu bamuyi da maganar nan da Fatima ba, na fara ganin canji daga wurin Yusuf, ya daina yawan kirana kaman yanda muka saba, koda yaushe na kira wayarshi busy, lokacin da nayi sa’a ya daga ne, bazai tsaya muyi magana ba, sai dai yacemun yana zuwa yanzu zai kirani,
Wani lokacin sai da dare yake kirana, wani lokacin ma na yi barci, haka zan wartsake in daga saboda ina son jin muryarsa, shima ba wani dadewa muke ba, idan na fara mishi korafi sai dai ya ba ni hakuri yace yanayin aiki ne, ga karin girman da aka mishi bayan dawowarshi.
Maganar zuwa gidanmu kam babu ita, tun bayan ranar nan daya dawo, sau daya ya kara zuwa, daganan ya dauke kafa.
Bani da wata kawar shawara bayan Fatima, itama na daina samunta a waya, koda yaushe Busy itama na mata uzuri saboda yawan samarinta, sai ban yi tunanin komi ba, gidan namu ma ta daina zuwa, daman itace ke yawan zuwa, in baka manta ba na fada maka daman ba son yawo ne da ni ba.
Yau dai shiryawa nayi da niyyar zuwa gidan nasu domin kai mata kukana, ganin har Ummi ta fara tambayana Yusuf, ganin yanda ya dauka lokaci bai zo ba.
A tsakar gida na tarar da Maminsu tana kokarin daura girkin dare, na gaishe ta ta amsa cikin fara’a,
“Ya Ummin taku?”
“Lafiya lau take, tace a gaisheku”
“Ina amsawa, bara in kira miki mutuniyar taki”
Ta kwala mata kira, “Kina ina Fatima? Ki fito ga Habiba”
Mamaki ya cikani, tunda nake zuwa gidansu Fatima, Maminsu ba ta taba mun haka ba, ita da kanta take cewa in shiga, idan naje gidan nasu kaman gidanmu haka nakeyi, ko ban isketa ba, sai in shige dakinta harta dawo.
Na shanye mamaki na na ce, “Bara in shiga ma Mami tunda tananan” Ta ce, “to” tana bi na da fara’a.
Shigata dakin nata, na tarar da ita da waya a kunne, tana fira cikin nishadi, da sauri ta kashe tana cewa, “Ina zuwa zan kiraka, nayi bakuwa yanzu”
Zama na yi gefen gadon, na dan kishingida, “kin ga don Tani dama kin gama shan soyayyarki, Mu’azzam dinne baza’a bani mu gaisa ba?” “Haba wanne Mu’azzam? Ai tun lokacin da mukai maganarnan dake nayi wuri na ajeshi, wani sabon kamu dai ne nayi”
“ke don Allah?” “wallahi fa” “koda yake, aike kullum daman cikin sabon kamu kike, Allah ya sa wannan din dai ya rikemun ke, Allah yasa dashi za’ai”
“Ameen fa, ai insha Allah shi dinne dai, don duk irin yanda na ke son mijin da zan aura ya kasance, hakan yake, kinga kuwa ruwan ido ya kare”
“Gaskia kam, shine kuma ko a waya ba’a bani shi mu gaisa? Allah ya sa ma kina bashi labarina, kar ayi auren ya hanamu zumunci” “Ke ma kinsan dole ne wannan, bari kafin ki tashi tafiya ma zan kirashi ku gaisa” “Ya dai kamata”
Na tattara natsuwata na maida kanta, na mayar da yanayin damuwa a fuskata, yanda zata fahimci halin da nake ciki, “Kawata akwai matsala fa.” “Ai da ganin yanayinki basai kin fada ba, meke faruwa ne?” “Ina da damuwa bayan ta Yusuf ne? Wallahi tun dawowarshi duk ya wani canjamun…….” Na kwashe duk halin da muke ciki na fada mata.
Tun kafin in gama fadi mata, itama yanayin ta ya koma na bacin rai, duk ta nuna alamun rashin jin dadin abunda ya ke mun, “anma gaskiya Yusuf bai kyauta ba, abunda zai mana kenan? wallahi ni duk raina ma ya baci”
“Ke ma kya fada kawata, anma kila da gaske yanayin aikin nashi ne”
“Yanayin aiki dai? Rainin hankali dai, da daya damu dake duk aikin da yake ai saiya samu lokaci ya kiraki, sai yanzu don rainin hankali? Da abunda yake nufi dai.” “Abunda yake nufi kamar me kawatah?” “Kila wata ya samu ko? Yake so ya yakice ki ta haka”
Saurin girgiza mata kai ta yi, “Gaskia Yusuf bazai mun haka ba.” “Bakisan halin maza bane akawata, kedai kici gaba da kama kanki, don yaga kina sonshi da yawa ne yake miki haka, kema wuri za ki yi ki aje shi, lokacin da yaga dama ya kiraki, ke ni banma ce ki kira shi ba, ko ya kiraki karki dauka, ki nuna mishi kema kina da aji, don yaga kina bibiyar shi ne, kina nuna damuwarki a kanshi zai ringa mi ki haka.”
“Kawata anyi haka? Karfa garin jan ajin, in koya mishi rayuwa babu ni.” “Tam zaunanan, ina baki kina kin amsa, kici gaba da shisshige mi shi yana wulakanta ki”
Na yi tagumi, “kinsan dai yanda nake son Yusuf, bani son rasa shi a rayuwata”. “Ba za ki rasa shi ba kawata, kedai ki ja ajinki kawai.”
“Tam shikenan, zan kokarta inyi amfani da shawararki kawata”. “Yauwah ko ke fa, in banda ma ya gama gane yanda kike son sa, meye na ki ringa kiransa yana kin dauka? Nifa tunda kikacemun yace zai kiraki bai kira ba ya gama bani haushi”
Jin dadi lullube a fuskata, kamar an yayemun rabin damuwa ta nake ji, “Gaskia Kawata shiyasa na ke sonki, ina jin dadin yanda kike mayar da damuwata taki, shiyasa duk duniya bani da kamarki” “haba ai wannan abun haushi ne, kedai ki kula da abunda na fada miki, shi da kansa zai kawo kanshi gida”. “Allah yasa, da ko naji dadi sosai.”
Mu ka shagala da firar mu kawai, tana kara nuna mun yanda taji haushin Yusuf, ni sai lokacin ma na fara jin haushin abinda ya ke mun, tana kara jaddamun in shareshi kar in nuna na damu dashi nima, har ta rako ni kofar gidansu tana kara fadamun, na tafi gida ni nama manta da maganar zata kiramun saurayinta mu gaisa.
Na dauka shawarar Fatima ta zauna daram a zuciyata, a da har so na ke dare ya yi Yusuf ya kirani a waya, bani barci saboda jiran wayarshi, anma yanzu silent ma nake sakata don ma kar inji shigowar kiranshi in kasa hakuri sai na dauka.
Kwata-kwata na daina zaga kiranshi, daman a chat ko na mishi magana sai yayi kwana biyu bai maidomun ba, nima sai na daina mishi, na nema wuri na ajjeshi, kamar yanda Fatima ta bani shawara, duk da dauriya kawai na ke.
Alhamdulillahi Shawarar Fatima tayimun amfani, da daya kira ni sau daya idan ban dauka ba shikenan, ya koma har sau biyu yana kirana, an ma duk da haka bani dauka.
Ranar daya cika sati na biyu da zuwa gidansu Fatima, ina kwance bayan ya gama kirana naki dagawa, sai ga Khadija ta shigo.” “Yaya Habiba, Ummi tace a faza miki Yaya Yusuf na falo yana jiranki.” Na tashi da murnata ina kallonta, “da gaske kike?” “Ehh wallahi.”
Mikewa nayi da sauri na feshe jikina da turare, na saka hijab ina ta sauri, na tafi inda ya ke. Kallonsa kawai da nayi, duk sai naji na kasa tuna wani laifi da yamun, gaba zaya laifin sa ya wanke a wuri na.
Na zauna kujerar da take kallon tashi, bayan na gaidashi, na kuma mishi sannu da zuwa, fuskata cike da jin dadin ganinshi. “Ina wayarki ina ta kira baki daga ba?” “Ta na can daki na saka Charge, banma ji ba”. “Fada mun gaskia dai, kina fushi dani shiyasa kika daina daga kirana ko?” “A’a wallahi, kaima kasan bazan iya fushi dakai ba”. “Saboda me?” “Saboda ina sonka da yawa mana.” Na rufe idanuwana bayan na gama fada mishi, ya dan tabe baki. “Ni ma ina sonki da yawa Habibatee, abunda ya saka ni zuwa yau ma kenan don ki nunamun kalar son da kikemun”
“Kamar ya fa?” “Kin tabbatar kina so na ba?” Na daga mishi kai, “duk abunda na nema a wurinki zaki ba ni?”
Ina dariyar yake na ce, “ni dinma taka ce ai, ballantana abunda na mallaka.” Har a zuciyata nayi wannan maganar, don wallahi yadda na ke kara jin soyayyar Yusuf a lokacin, ji nake koda kaina ya ce zai yanke ya siyar, bar mishi zanyi indai zai tabbatar da son da nake mishi.
Mikewa ya yi daga kujerar da ya ke, ya dawo inda na ke, gabana ya fara faduwa ganin ya zauna kusa da ni.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!