Connect with us

WASANNI

Liverpool Ta Na Bukatar Lashe Dukkan Wasanninta, Cewar Salah

Published

on

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Mohammad Salah, ya bukaci ‘yan wasan kungiyar dasu cigaba da dagewa kuma su mayar da hankali wajen ganin sun lashe ragowar wasanninsu domin daukar kofin firimiya.
Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta casa Chelsea daci 2-0, abinda ya ba ta damar ci gaba da zama a teburin gasar firimiyar Ingila da maki 85, yayinda Manchester City da ke matsayi na biyu da maki 83 inda Sadio Mane da Mohamed Salah ne suka ci wa Liberpool kwallayen nata guda biyu.
Kocin Liverpool, Jurgen Kloop ya jinjina wa Salah, yana mai bayyana shi a matsayin jigon cikar burin kungiyar na ganin ta lashe kofin a karon farko cikin shekaru 29 haka zalika Klopp ya yaba wa Salah game da kwallo ta biyu da ya jefa a ragar Chelsea, kwallon da ya ce, ta matukar kayatar da shi.
Ita ma Manchester City ta samu nasarar doke Crystal Palace da ci 3-1 a wasansu na ranar Lahadi kuma yanzu haka wasanni biyar suka rage wa Manchester City, Liverpool kuwa, nada sauran wasanni hudu. Kowacce daga cikin kungiyoyin biyu na fatan ganin ita za ta lashe kofin a bana.
Sai dai akwai wasanni masu zafi a gaban Manchester City da suka hada da haduwarta da Manchester United da Tottenham, kungiyoyin da ke da karsashi matuka, sabanin Liverpool da za ta kara da Cardiff da Huddersfiled da Newcastle da kuma Wolves.
Har ila yau Liverpool da Manchester City har yanzu suna buga gasar cin kofin zakarun turai kuma a gobe Liverpool zata kai ziyara kungiyar kwallon kafa ta FC Porto yayinda Manchester City zata karbi bakuncin Tottenham.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!