Connect with us

TATTAUNAWA

Na Hada Gidan Rediyon Da Ake Ji A Jahohi Takwas – Abdullahi Na’ura

Published

on

ABDULLAHI YAKUBU WUNTY, Wani mutum ne da Allah ya yi masa baiwa na gyaran rediyo da kuma iya hada gidan rediyo har ya calla na’urarsa a ji sautin a jahohi da dama a cikin kasar nan. Abdullahi Na’ura ya taba hada gidan rediyo mai suna ‘Wunty Rediyo’ a cikin Bauchi, a lokacin da ke hada shirye-shiryensa ana jinsa a ko’ina a fadin jihar. Nijiriya dai za mu iya cewa tana da masu baiwa samun zarafin baje fasahar sune kawai ba su yi ba. Idan ka ganshi za ka sha mamaki a ce maka mutum irin wannan na da baiwar hada wani abu. Abun mamaki ne idan ka ga abubuwan da yake hadawa har a jisa. To ko mene ne wadannan abubuwan ku biyu domin ku je. KHALID IDRIS DOYA ne ya tattauna da shi kamar haka:

Da wa muke tare a yanzu?
Sunana Abdullahi Yakubu Wunty, wanda aka fi sani da suna Abdullahi Na’ura. An haifeni a cikin garin Bauchi yanzu ina da shekaru 53 a duniya. na yi makarantar firamare da sakandari, na fara karatuna ne a makarantar firamare ne a Shadawanka, Bauchi (a da ana kiranta da suna Semful) daga 1973 zuwa 1079. Daga bisani na tafi sakandari GSS Gumau a 1980, a 1982 ne kuma na yi taransfa na koma Comprehensibe Day Secondary School da ke Bauchi. ni dai ban kai ga kammala sakandarin ba ma ka ji yanda aka yi.

Ta yaya ka fara harkar gyare-gyaren rediyo kuma har ka zo ka fara tunanin hada gidan rediyo da watsa shirye-shirye?
Eh to gaskiya ni tun ina dan firamare na ke koyon aikin gyaran rediyo, akwai wani mutum ana kiransa da suna Alhaji Tawakkaltu yanzu haka yana kasar Ogomosho a wajensa na koyi aikin gyaran rediyo. Tun a haka, ina dai gyaran rediyo kullum sai na ke cewa ni fa zan yi gidan rediyo, ni ma na hada abun da zan ke fada har a ji muryana a ji kuma sautin gidan rediyona a cikin rediyon nan da na ke ganinta a gidan kowa. Ta kai idan na kawo rediyo kusa da ni ina gyara, misali ina gyara daya ina kuma jin rediyo da daya ko BBC ko Amurka hakan nan sai idan ina murda dayan sai na ji sautin dayan na shiga cikin dayan, a bisa wannan sai na ce to mene ne ya sanya sautin wannen ke shiga cikin wancan rediyon, daga nan sai na fadada bincike. kullum dai ni ina fadin zan yi gidan rediyo a haka.
Wata rana Allah sai ya taimakeni a wata rana (ba zan mance ta ba) ranar 25 ga Febrairu 1980 ina cikin gwada sa’a ta, ina dai da burina, ina cikin murda tashar rediyo bayan da na zabi Firikonsi din ina ta kan murdaya sai na yi nasara na kama tashar da babu kowa a kan layin sai na daura nawa a kai, bayan da na fara samun haka sai na dauki makilfon dina sai na hada. Da na hada idan na ce Hello sai na ji hade-hadena ya amsa da cewa ‘AAaa’ ba zan ji sauran ba, har aka zo ina jin haa amma ba zan ji sauran ba. ina dai ta ci gaba da tunanin ya za a yi na kirkiri gidan rediyona na kaina, na dau lokaci sosai Ina wannan faman.

To yaya aka yi ka samu nasarar kirkirar taka rediyon?
A wannan yanayin da na ke cikin, wata rana na zo hutun makarata lokacin ina Gumau sai na ji labarin ai akwai wani wanda ya hada gidan rediyo a wani kyauye da ake kira Fingel, nan da nan na tashi na kama hanya na nufi Fingel domin ganin wannan mutumin, kai bar ka ji ma da kafa na taka na je wannan kauyen. Na je kauyen na kuma hadu da wannan mutumin na kuma ga gidan rediyon da ya kirkira (amma gaskiya na mance sunansa, shi mutumin kenan ba). bayan da na je aka kunna min rediyon na ga yanda ya hada, ni ma dawowata ke nan sai na zo ina ce musu zan yi gidan rediyo, zan yi gidan rediyon. Ina zuwa sai na dukufa. A da akwai irin time tebul da ake amfani da shi na rediyo da na samu. Nan da nan sai na harhada komatsena sai na samu zarafin fidda gidan rediyo, karin farko waka kawai na ke sakewa. Nan da nan sai jama’a suka fara tururuwa suna zuwa suna tambayar shin wai wani gidan rediyo ne suke sanya kida amma babu magana? Lokacin ma ba a san gidan rediyon nawa ba; kawai sakewa na fara yi jama’a suna ji, a lokacin ina watsa waka amma wallahi a lokacin ban san ya zan yin a hada ya yi magana ba, amma dai na fara samun nasarar ana jin waka. A lokacin ma tun wakoki irin su da irinsu ONAYO-ONAYO, Irinsu KASKARA-KODIN a 1980 ne na fara watsa wakoki a gidan rediyon. Bayan nan na zo na ina ta fama dai har Allah ya taimakeni na samu wani tab-recorder, na zo na hada shi ina cikin joni-joni dina, ina kan hadawa har Allah ya bani basirar da na samu yanda zan yi magana a ji, kuma na yi maganar kowa yana ji. Nan take idan zan yi magana sai na ce jama’a kuna tare ne da Wunty Rediyo. Nan da nan sai jama’a suka fara tambaya. Akwai wani dan uwan babana ya zo ya samu Babana ya ce masa ka ji Audu ya hada agidan rediyo ko? Kowa sai mamaki yake yi.

Daga nan sai aka yi yaya Na’ura?
Ai, ina baka labari, daga wannan lokacin duk gari ana jin gidan rediyo na, sai na fara fita da rediyo ina zagawa ina ne ake jina ina ne ba a jina. Da fari dai gidan rediyon nawa sai na hadashi da wani dabara sai a ji. Har na zo na fara samun dabarar yanda za a jini a ko’ina.

Wani mataki ne aka fara jinka a tasharka?
A da kamar yanda na fada maka, da fari sai na hada antenna rediyon da rediyon sai a ji, kai da, da fari ma a dakina kadai na ke jin abun da na ke watsawa, har Allah ya bani basira na sake samun yanda zan yi a jinni a waje, domin na samu dabarar yanda zan fitar da antena dina zuwa wajen, kai tafiya a hankali har ya zo ka zama jahohi takwas suna jin tasha dina na Wunty rediyo a wancan lokacin.

Na sani gidan rediyo ana watsashi ne da irin su Firikonsi da Kilohaz, mita ko wani abu makamancin hakan, kai ya aka yi naka babu wannan amma ana jinka?
Kai wallahi da yawan mutane idan sun zo sun ga yanda gidan rediyo dina yake sai su kama cewa ‘Abun mamaki’, wasu kuma ce Majik ne, wasu su ce tsafi ne. kai tsaye na kan ce musu ba tsafi bane. Baiwace wacce Allah ya yi min, dukkanin rediyon da na samu zan iya amafani da ita na sarrafa ta ta fara watsa shirye-shirye. A cikin minti biyar zan iya hada rediyo na dawo da shi ritansimita a fara jinsa duk gari.

Duk gari fa ka ce kuma a cikin minti biyar?
Kwarai da gaske, yanzu a yanda muke da kai din na, a wannan reburin idan na baje na’urorina a cikin kankanin lokaci zan iya calla tashata a ji ta, kai ni har ma rediyon da za a iya hadawa a sanya a aljihu take yada shirye-shirye na iya hadawa yanzu haka ina da su a ajiye. Hatta a jikin wayar hanset ina iya hada gidan rediyon, yanzu haka ma ina da wanda na hada a gidan rediyo daga rediyo.

To yanzu ya ka ke ka yi?
Na farko ina neman kwamfunet na rediyo, irin su tiransisto da irin su rizisto. Tiransisto wani abu ne yana nan mai kafa uku ne, amfaninsa ko aikinsa a jikin rediyo yakan yi amfuryeyin ne na abun da ka hada masa, akwai wajen sanya abu , nan ne ake sanya masa abu, sannan yana da wajen amsar abubuwan da aka hada masa. Amfaninsa ke na da yawa.

Baya ga wadannan abubuwan akwai abubun da kake nema kafin rediyonka ta yi aiki?
Eh akwai, akwai ariya, bayan ariya sai makilfon, da kuma kebul shi kenan sai rediyo na ta fara aiki. Ni kowani irin ariya na kan iya hadasa ya zama antenna.

Wani irin antena da ka yi amfani da shi har ake jinka a dukkanin fadin Bauchi?
Irin antenna na nan a jikin jikin sakatariyar karamar hukuma Bauchi, da ina watsa shirye-shiryena karamar hukuma ta bani wani waje ina hade-hade na amma wani mai kudi ya zo ya mallake shawo (wakilinmu ya sake sunansa don wasu dalilai) ya hade shagon da aka bani ina hade-hade na, har yanzu kuma antenna da na ke amfani da shi na sama. Ko yanzu na je na hada zaka ji ni a dukkanin fadin jihar Bauchi, da sauran jahohi sama da takwas.

Ya maganar Firikonsi?
Eh na zaba na kai wajen masu sahalewa suka amince suka duba suka bani izinin ci gaba da amfani da wannan firikonsin da na zaba. A lokacin Naitel sune suke bada izinin amfani da firikonsi na rubuta na basu a lokacin Alhaji Maina ne shugaba na ci gaba da yin amfani da firikonsin.

Mene ne firikonsin ka din?
Firikonsi dina shine 14.00kilohaz midiyon web ban. Sunan rediyona Wunty rediyo.

Yanzu idan aka ce ka je wajen wani taro ka hada rediyonka ana ji a duniya za ka iya?
Kwarai kuwa, sosai ma cikin kankanin lokaci ma. Zan hada a jinni a kowani waje idan na ga dama.

To da me da me kake bukata kafin ka hadan?
Kawai abun da na ke bukata shi ne tiransisto, rizisto da kafasto da kuma irin su tirasfoma da zarar na samu irin wadannan abubuwan an gama magana zan hada maka gidan rediyo, abubuwan da zan nema bayan haka kadan ne.

Da wutar lantarki ko jannereto kake amfani ko yaya?
Na kan hada gidan rediyo na da batir ma, ina amfani da wuta da sola ma idan ina so. Dukkani ina amfani da hakan.

Da yake kana aiki a gidan rediyon BRC ne a halin yanzu, shin kana da burin inganta gidan rediyon musamman ta fuskacin na’urori?
Tabbas ina da burin hakan, amma gaskiya gidan rediyon Bauchi na bukatar sabbin kayan aiki na zamani ne. amma muna da burin kai gidan rediyon babban matsayi.

Ga shi dai ka bayyan wadannan abubuwan, shi baiwa ne ko kuma iyawa ne?
Gaskiya akwai baiwar ma, akwai iyawa din ma. Domin ni tun ina dan aji hudu a firamare na ke koyon gyaran rediyon. Na kuma koya na koyar da wasu.

Daga cikin wadanda ka koyar akwai wanda ya iya hada rediyo kamar kai?
A’a gaskiya, dukkaninsu babu wanda ya iya hada rediyo, amma dai sun iya gyara sosai.

Yanzu idan ina son koya min yanda zan hada gidan rediyon zaka iya?
Eh zan koyar maka. Misali yanzu idan ka nemi gidan rediyonka, guda biyu, sai ka fara neman layin da babu kowa a kan firikonsi, sai ka zaba, bayan ka zaba za ka ji wani abu ya yi maka ausaloshin za ka ji ya zaba, kamar tasha ta bude amma ba ta fara magana ba, a wannan lokacin ne za ka nemi hanyoyin da za ka hada tab dinka yanda kowa zai jika.

Ka ce ana jinka a jahohi kusan takwas idan ka kunna rediyonka, ba ni misalinsu?
Tabbas idan na kunna, ko kuma na ce maka lokacin da na ke kunnawa, ana iya jina a Kano, Adamawa, Gombe, Taraba, Jos kai har kasar Nijer ana jin tashata. Kuma wallahi idan na hada ka zo ka ga wajen da kuma na’ororin idan aka ce maka wannan tashar ne ake jin kaza sai ka musa, kada kuma ka musa domin haka abun yake. Da yawan ‘yan jarida sun yi aiki a gidan rediyona, sun iya ta wakoki da gaishe-gaishe da kuma wasan kwaikwayo duk na sha yi.

Ka ce kana da antenna a sakatariya mene ne ya kaika wajen?
Eh da shagona ne a wajen, ina hada shirye-shiryena. Amma an amshi shagon a wajena, sai na zo na bar shawo, amma yanzu haka ina son idan na yi ritaya na kammala aikin gwamnati zan hada gidan rediyona na ci gaba da watsa shirye-shiryena.

Mene ne burinka a rayuwa?
Burina na ga na koyar da wasu daga cikin ‘yan kasar nan gyara da fasahar zamani kuma suna yi. In na kammala aiki zan bude gidan rediyo da kai. Yanzu haka ina da burin gidan rediyon da ke hanu na inganta shi, idan na kammala aikin zan nemi shawo na ci gaba da watsa shirye-shiryena na kaina.

Misali da za ka samu karfafawa daga gwamnati ko wasu kungiyoyi shin zaka bunkasa wannan gidan rediyon ka?
Da zan samu hakan sai na hada tashar da babu irinsa a yankin nan, Nijeriya ma sai ta yi daker ta samu gidan rediyon da zai kai nawa. Domin na san abubuwa sosai a kan rediyo kuma baiwace. Ina da wata naura da na hada da kawai da ita na ke jone-jonena sai ka ji cal ana jin muryata.

Bayan gidan rediyon Bauchi BRC akwai idan ka taba zuwa aka yi aikin naurori ne?
Akwai gidajen rediyon da yanzu haka ina daga cikin wadanda suka jera na’urorin ciki da yawa, kuma na sha zuwa taruka da bita kan naurori da sauransu domin bunkas gami da kara samun ilimi kan na’ura.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!