Connect with us

RAHOTANNI

NFBCB Ta Kwace Finafinan Batsa Na Naira Bilyan Biyu

Published

on

Hukumar tantance Fina-finai ta kasa, ta bayyana cewa, ta kwace fina-finan batsa da makamantan su da suka kai kimar Naira bilyan biyu, a cikin shekaru biyun da suka gabata, mukaddashin daraktan hukumar ce, Bola Athar, ta bayyana hakan.
Ta bayyana hakan ne cikin wata tattaunawa da ta yi da kamfanin dillancin labarai na kasa a wajen wata liyafar cin abincin dare wacce aka shirya ta domin taya babban shugaban hukumar, Mista Adedayo Thomas, murnar cika shekaru biyu a kujerar shugabancin hukumar ranar Lahadi, a Abuja.
Manyan jami’an gwamnati da na hukumar, masu ruwa da tsaki a kamfanonin kasar nan da sauran manyan baki duk sun halarci liyafar domin taya Mista Thomas murna a kan yanda ya jagoranci shugabancin hukumar ta tantance fina-finai cikin shekaru biyu.
Athar, wacce ta yi nazarin gagarumin ci gaban da aka samu a hukumar a lokacin da take magana, ta ce, ci gaban da aka samu ba shi da abin kwatanci.
A cewar ta, kayan da hukumar ta kwace a daidai lokacin da ake maganan sun hada da, kasusuwan DBD, CD irin masu daukan fina-finan batsa har kala 20 a cikin kaset guda, da kuma wasu fina-finan waje da ba su dace da al’adunmu ba, har ma da wasu na batsan da a nan cikin gida ne aka shirya su.
“Wannan shi ne karo na farko a tarihin wannan hukumar ta NFBCB, inda aka sami babban daraktan hukumar yakan fita aikin kama haramtattun kaya da kansa, a cikin shekaru biyu hukumar ta sami tsarkake kasuwar fina-finai daga fina-finan da ba su dace ba, da har kimar su ya kai Naira bilyan 2.5.
“Kayan da muka kwace sun hada da su fina-finan batsan kansu, na gida da na waje, da kuma mashinan da ake amfani da su wajen yada fina-finan.
“Mun kwace wadannan kayayyakin ne a lokacin da muka tashi tsaye a kan aikin namu a duk sassan kasar nan, da suka hada da, Kaduna, Benin, Warri, Kano, Onitsa da Legas, mun yi wannan ne domin ya kasance jan kunne ga masu sarrafa irin wadannan fina-finan da masu siyar da su a kasuwa,” in ji ta.
Athar, ta bayyana cewa, duk wadanda aka kama a lokacin samamen da suka kai, tuni hukumar ta gurfanar da su a gaban kotuna, kamar yanda dokar da ta kafa hukumar ta tanada.
Ta ce, hukumar kuma ta karfafa alakar da take da ita a tsakanin ta da hukumar ‘yan sanda da sauran masu ruwa da tsaki, wanda dangantakan na su ta haifar da da mai ido.
Aikin hukumar ne dai ta yi rajistan duk wani fim da bidiyoyi a ko’ina cikin kasar nan, da makamantan hakan.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!