Connect with us

LABARAI

Shugabancin Majalisar Ta 9:  Wakilan Jam’iyyarmu Na Da ’Yancin Neman Hadin Kan ’Yan Adawa – APC

Published

on

Jam’iyyar APC ta ce, ba ta sukan wakilanta a Majalisar kasa da su shiga tattaunawa da wakilan jam’iyyan adawa ta PDP a kan abin da ya shafi shugabancin majalisar na 9.

Sanarwar da Kakakin jam’iyyar na kasa, Malam Lanre Issa-Onilu, ya fitar tana cewa, irin wannan tattaunawar ba bakuwa ce ba a tsarin dimokuradiyya.

Malam Lanre Issa-Onilu ya ce, sabanin rahotannin da wasu kafafen yada labarai ke yadawa, wakilan jam’iyyar APC a yanzun haka suna cikin tattaunawa da sauran wakilai na jam’iyyun adawa, wanda hakan kuma bai sabawa tsarin mulkin jam’iyyar ba.

“APC tana da isassun wakilai mafiya yawa a duk majalisun biyu, don haka, muna da yawan da za mu iya fitar da shugabanni a majalisun,” in ji shi.

Ya yi nuni da cewa, tsarin dimokuradiyya ya yi na’am da mahimmancin ‘yan adawa, musamman ma dai in har ba ka da kashi daya bisa uku, wanda ake da bukata a wasu lokuta na musamman.

Sai dai, Issa-Onilu ya ce, jam’iyyar APC a matsayinta na jam’iyyar da ke mulki ta fahimci cewa, lafiyayyar majalisar kasa da ta dace za ta karfafa ikon da take da shi na yi wa ‘yan Nijeriya aiki.

Issa-Onilu ya ce, kwanan nan jam’iyyar ta APC za ta fitar da tsarin ta na rabon mukamai da kuma abin da ya shafi shugabanni da sauran masu fada a ji a cikin majalisun na kasa guda biyu, da za su shugabanci zaman majalisar na 9.

Ya ce, kwanan nan ne jam’iyyar za ta bayyana matsayinta a kan shugabancin majalisar Wakilai ta kasa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!