Connect with us

LABARAI

Sojoji Sun Kashe ‘Yan Boko Haram 27 Da Kwace Makamai

Published

on

Sojoji na Sector 1 na Operation Lafia Dole, da hadin gwiwar rundunar sojojin Kamaru sun yi kokarin dakatar da hare-haren ‘yan ta’addan Boko Haram a lokacin da su ka kawo mummunan hari a yankin Chadi.
A cikin wata sanarwar da aka bayar jiya Litinin mataimakim Darankta Janar Kanar Sagir Musa, ya bayyana cewa “harin da yan ta’addan wanda ya faru a Arewacin Wulgo, Tumbuma, Chikun.
A cewarsa, lokacin da jami’an mu suka tunkari ‘yan ta’addan 27 daga cikin su, sun raunana kuma an yi nasarar kwato wasu makamai daga hannun su.
Cikin abubuwan da aka kwato daga hannun su sun hada da bindiga kirar AK 47,manyan makamai na’urori, 4 bindigo guda 1,000 launi daban -daban.
“Babu abinda ya samu sojojin mu da kuma na sojojin Kamaru.”
Ya kara da cewa “ Jami’an mu suna nan a yankunan Gombaru, Ngala domin tabbatar da tsaro a yankin sabida mun dauki alwashin kawo karshen wadannan yan tawayen.”in ji Colonel Musa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!