Connect with us

KASASHEN WAJE

Sojojin Chadi Sun Kashe ‘Yan Boko Haram 63

Published

on

A kalla mayakan Boko Haram 63 sun rasa rayukansu a wani dauki-ba-dadi da sojojin Chadi a cikin daren da ya gabata.
Mai magana da yawun sojin kasar, Kanar Azeem Bermandoa ya ce, an kashe musu jami’ai bakwai tare da jikkata 15 a harin da mayakan na Bokio Haram suka kaddamar kan sansanin sojin da ke Bouhama a yankin Tafkin Chadi.
Bermandoa ya kara da cewa, a halin yanzu suna kan farautar sauran mayakan na Boko Haram bayan sun kashe 63 daga cikinsu. Ko a watan jiya, sai da Boko Haram ta kashe sojoji 23 a Yankin Tafkin Chadi, harin da ake kallon sa a matsayin mafi muni da kungiyar ta kai kan dakarun sojin Chadi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!