Connect with us

LABARAI

Talauci Na Da Tasiri A Kwakwalwar Yara – Bincike

Published

on

Wani sabon bincike kan illar talauci ya nuna cewa, kwakwalwar yara ‘yayan talakawa, wadanda iyayensu basa da wadataccen karatu, kan zama rarraunaar kwakwalwa a kan ‘yayan masu kudi, sannan sun fi yiyuwar zama wani iri a rayuwarsu.
Farfesa John Spencer tare da abokan aikinsa, daga jami’ar karantar halayyar dan adam, ‘East Anglia School of Psychology’ ne ya jagoranci gudanar da binciken kan karfin kwakwalwar yara ‘yan wata 4 zuwa shekara 4.
A yayin gudanar da binciken, sun yi anfani da nasu sakamakon binciken, inda suka kwatantashi da yaran kasar Amurka, binciken ya nuna masu cewar ‘yayan da suka fito daga gidan talakawa sun fi karancin kwakwalwa, sannan sun fi yiyuwar samun matsala a rayuwa (lalacewa).
Farfesan ya bayyana cewa, “A kowace shekara, ‘yayan talakawa da kuma masu matsakaicin hali kan gaza kai matakin ci gaba na rayuwa da ya kamata a ce sun kai a ka’ida, wanda hakan ya sanya bukatuwar sanin illar talauci a cikin rayuwar yara masu tasowa.”
Farfesa ya ci gaba da cewa, “Binciken da aka gudanar a baya sun nuna cewa talauci da wahalhalun rayuwa na da tasiri sosai a kwakwalwal yara, inda hakan ke haifar da kakkausan hali da mummunan zuciya. To sai dai, kalilan ne daga cikin bincike suka yi duba ya zuwa ga yanda kwakwalwa ke aiki a lokacin girma.”
“Burinmu shi ne kara yin duba da zufafa bincike kan karfin aikin kwakwalwar yayan talakawa, domin gano dalilin da yasa da yawadaga cikin ‘yayan talakawan, basa kaiwa matakin ci gaban rayuwa da ya kamata su kai,” inji Frafesa Spencer.
Wannan bincikenn dai, matakin farko ne nan kokarin ganin yanda za a kara inganta kwakwalwar yar da kaifin ta tun gabanin su fara cimma wahalhalun rayuwa da matsaltsalun yau dakullum, inji shi.
Daga cikin abubuwan da aka kula da su yayin gudanar da binciken akwai: ilimin iyaye, kudin shiga, adadin ‘yaya a gida, kabila, addini da kuma karfin tattalin arziki.
Sakamakon binciken ya nuna alakar talauci da kaifin basira na kwakwalwa da tarbiya, inda aka ce, ‘yayan talakawa sun fi samun raunin fahimta da rashin karfin kwakwalwa, da kuma jin rashin muhimmanci ko anfani.
“Ko da yake dai, wahalhalun duniya da talauci kan iya sanya yara su kasance cikin layin talauci har tsawon rayuwarsu, to amma dai kuma duba ga yanayin canji da ci gaban da kwakwalwa kan samu, hakan zai zama wani fata ga samun canji ga ‘yayan talakawa.”
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!