Connect with us

LABARAI

Yadda Mu Ka Galabaita Boko Haram A Karshen Mako, Cewar Rundunar Soja

Published

on

Da safiyar Litinin ne sojojin Nijeriya tare da hadin gwiwa da na kasar Kamaru, wadanda ke aikin samar da tsaro a karkashin rundunar Lafiya Dole, a yankin Arewa Maso Gabas, sun bayyana cewa sun halaka mayakan kungiyar Boko Haram 27 a wani samame da su ka kai ranar Asabar.
Sanarwar mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na rundunae, Kanal Sagir Musa, ya ce maharan sun gamu da ajalinsu ne a wani taho-mu-gamu da gamayyar sojojin a samamen kakkabe ’yan sari-ka-noken a arewacin jihar Borno a kauyukan Wulgo, Tumbuma, Chikun Gudu da Bukar Maryam.
Bugu da kari kuma, ya kara da cewa, dakarun sojan sun yi nasarar gano motocin yaki guda biyar da baburan hawa, tare da manyan bindigogi biyar kirar AK-47. Sauran sun hada da bindigogi masu sarrafa kan su kala daban-daban, makamin roka na GPMG da bindiga mai harbo jirgin sama guda biyu da makamantansu a hannun mayakan Boko Haram.
“Wanda kuma babu rasa rai a bangaren sojojin Nijeriya da na Kamaru. Yayin da kuma wannan gamayyar kai samamen zai ci gaba da gudana kamar yadda a ka tsara shi, musamman a yankin Gombaru-Ngala, inda wadannan maharan ke kaura zuwa can, ta hanyar amfani da runduna ta kasa da kasa a shirin su mai taken ‘Samamen ’Yanto Tafki’, domin zakolo maharan daga inda su ka buya,” in ji shi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!