Connect with us

RAHOTANNI

Yaki Da ‘Yan Ta’adda Yana Kara Samun Goyon Baya

Published

on

Gwamna Abdul’aziz Yari na Jihar Zamfara, ya umurci shugabannin hukumomin tsaro a Jihar da su afka filin daga domin karawa da ‘yan ta’adda, tun da dai rundunar ‘yan sanda ta kore batun yiwuwar yin zaman sasantawa da ‘yan ta’addan.
Yari ya shaidawa manema labarai hakan ne a karshen zaman majalisar tsaro ta Jihar wanda aka yi a gidansa da ke Talatan Mafara.
Zaman majalisar tsaron wanda aka fara shi tun a ranar Asabar, a gidan gwamnati da ke Gusau, an karkare shi ne ranar Lahadi a gidansa da ke Talatan Mafara.
“Muna son mu kara kaimi ne, mun kuma tsayar da shawarar a yanzun haka jami’an tsaronmu suna gab da cimma nasara a fagen dagan.
“Tabbas, ba wata mafaka a halin yanzun ga ‘yan ta’addan. Ina son na tabbatar wa da al’umman Nijeriya da ma na Duniya baki-daya, ayyukan ta’addanci da makamantan su suna gab da zama tarihi a Jihar Zamfara.
“Za mu kafa sansanoni a duk wuraren da ‘yan ta’addan suke, ta yadda auka masu zai zo mana cikin sauki.
“Za kuma mu aike da irin wannan sakon ga duk Jihohin da abin ya shafa, Kebbi, Katsina, Kaduna, Kano, Sakkwato da Neja, ta yanda za mu hada kai mu rika tunkarar ‘yan ta’addan a lokaci guda,” in ji Yari.
Gwamnan ya yabawa hanin da aka yi na masu aikin hakan ma’adinai a kwanan nan a cikin Jihar, wanda gwamnatin tarayya ta yi, ya yi nuni da cewa, hanin ya kara cisgunawa ‘yan ta’addan da kuma maboyar su.
“Mun gano cewa, akwai alaka a tsakanin ‘yan ta’addan da masu tonon ma’adinan, saboda wasu daga cikin mutanan da aka sace sun bayar da rahoton cewa an ajiye su ne a wuraren da ake tonon ma’adinan.
“Gwamnatin Jihar ba ta taba amfana daga haraji ko wata kyauta ba daga masu tonon ma’adinan, don haka ba wani abu da suka amfanar da mu da shi na ganin ci gaban wannan Jihar,” in ji Yari.
Hakanan, Kwamishinan ‘Yan sanda na Jihar ta Zamfara, Mista Celestine Okoye, ya ce, sam jami’an tsaro a Jihar ba za su shiga wata tattaunawa ba da ‘yan ta’addan kamar yanda Gwamnan Jihar ya umurci jami’an tsaron da su shiga karon batta da ‘yan ta’addan.
Okoye ya fadi hakan ne a ranar Lahadi, a Talatan Mafara, lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan zaman majalisar tsaro ta Jihar.
“In har ka ji ana maganar a tattauna, hakan yana nufin tafiyar ba ta yi nisa ne ba. Duk kafofin tattaunawar mun rigaya mun toshe su.
“Ya kamata ‘yan ta’addan su san cewa a yanzun za mu tunkare su ne da duk karfinmu, don haka babu wata matsera a gare su.
“Kwanan nan, ayyukan ‘yan ta’adda zai zama tarihi a Zamfara, amma ba zan bayyana matakan da za mu dauka ba a nan,” in ji shi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!