Connect with us

WASANNI

Za Mu Iya Maimaita Abinda Mu Ka Yi A PSG – Rashford

Published

on

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Marcus Rashford, ya shawarci ‘yan wasan kungiyar dasu sake dagewa domin ganin sun maimaita irin abinda sukayi a Paris Saint German sai dai yace dole sai sunyi aiki tukuru.
Tsohon dan wasan Barcelona, Aledis Sanches, wanda ya zura kwallaye 41 cikin wasanni 141 daya bugawa kungiyar yana daya daga cikin ‘yan wasan da zasu iya buga wasan yayinda dan wasa Nemanja Matic shima yadawo kuma aka tafi dashi kasar ta Sipaniya.
Rabon da Sanches ya buga wasa a Manchester United dai tun ranar 2 ga watan Maris da suka lallasa Southampton daci 3-2 yayinda kuma Matic rabonsa da buga wasa shima tun wasan da suka doke kungiyar Watford 2-1 a ranar 30 ga watan na Maris.
Shi ma dai dan wasa Luke Shaw, dan baya na kasar Ingila an tafi dashi duk da cewa bazai buga fafatawar ba sakamakon katin gargadin da aka bashi a wasan farkon da suka buga a filin wasa na Old Trafford a satin daya wuce.
“Dole za mu dinga tuna abinda yafaru a wasanmu da PSG amma yanzu dole mu gane cewa wasan PSG yanada banbanci da wasan Barcelona saboda kalar wasan daban kalar filin wasan daban sannan kuma kalar ‘yan wasan daban’ in ji Rashford
Ga jerin ‘yan Wasan da Manchester United ta tafi dasu wasan Barcelona: Dabid De Gea, Sergio Romero, Lee Grant, Diogo Dalot, Matteo Darmian, Ashley Young, Phil Jones, Bictor Lindelof, Marcos Rojo, Chris Smalling, Luke Shaw, Fred, Nemanja Matic, Scott McTominay, Andreas Pereira, Paul Pogba, Jesse Lingard, Juan Mata, Anthony Martial, Aledis Sanchez, Romelu Lukaku, Marcus Rashford.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!