Connect with us

LABARAI

Zagayen UEFA: Yau Dan Wasa Carles Puyol Zai Zo Tallen Giya Najeriya

Published

on

Fitaccen dan wasan kwallon kafar nan kuma tsohon dan wasan Barcelona, wato Carles Puyol, zai bayyana Najeriya a yau din nan, domin halartar zagayen da a ke yi da kofin zakarun Turai.
Puyol zai iso Najeriya ne a matsayin ziyarar kwanaki uku bisa gayyatar da kamfanin giya na Heineken su ka yi ma sa, don ya jagoranci tattakin gasar zakarun Turai din, saboda ya taimaka wajen sake hada dankon zumunci tsakanin mashaya giyar da kuma ma’abota kallon kwallon kafa.
Tsohon kyaftin din na Barcelona zai je garin Uyo domin halartar taro da mashaya giyar ta Heineken, inda za a gudanar da wani wasan kwallo, inda zai buga kwallo a matsayin kyaftin din Tawagar Shugaba tare da tsofaffin ’yan wasan Najeriya da masu shirya wasannin kasa da ’yan wasan Akwa Ibom da kuma wasu daga cikin kwastomomin da a ka zabo, wadanda za su kara da tawagar Shine Shine Bobo, wacce tsohon fitaccen dan wasan Najeritya, Jay Jay Okocha, zai jagoranta a matsayin kyaftin shi ma.
A ranakun 17 da 18 ga Afrilu kuma za mu ga Puyol a birnin Ikko, wato Lagos, inda zai yi kewayen ziyara da tattaki, kamar yadda a ka tsara da nufin janyo hankalin mashaya, don karkara tunaninsu ga giyar Heineken.
An kuma bayar da wata dama ga masu son a ba su tikiti kyauta, inda za su iya amfani da hashtag din #Unmissable, domin cimma burin hakan ba tare da biya ba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!