Connect with us

TATTAUNAWA

Da Kano A Ke Koyi A Siyasar Arewa, Cewar Malam Ibrahim Khalil

Published

on

MALAM IBRAHIM KHALIL shi ne shugaban majalisar malamai ta jihar Kano, amma ya dauki wani salo wanda malamai a Najeriya ba su cika daukar irin wannan salo ba; salon kuwa shi ne a tsunduma a cikin harkokin siyasa kai-tsaye, inda ya kasance dan jam’iyyar APC kuma daya daga cikin wadanda a baya a ka sa rai za su nemi kujerar gwamnan jihar musamman a 2011 da 2015, amma ya dakatar da hakan. A wannan tattaunawar da wakilin LEADERSHIP A YAU LAHADI, MUSTAPHA IBRAHIM TELA, fitaccen malamin ya yi hannunka-mai-sanda kan samar da alkibla guda daya, wacce Arewa ya dace ta bi tafarkinta, don kauce wa rarrabuwar kawuna a yankin da kuma samar da cigabansa mai dorewa. Ga yadda hirar ta kasance:

Malam, me zai ka ce game da halin da Arewa ke ciki a yanzu?
Babban abinda ya zama wajibi mu ja hankalin kanmu da kanmu shi ne, mutanen Arewa su samar wa da kansu alkibla sahihiya da kuma jagoranci sahihi. Haka kuma malaman addini su ja wa kansu kima ko kuma su kara wa kansu kima ko su tsare kimarsu ko martabarsu ko darajarsu, sannan su kuma ’yan siyasa lokacinsu ya yi da ya kamata su sani duniya yanzu ba siyasar hauma-hauma da siyasar barababiya ce abar yi ba ko siyasar biya wa kai bukata, a’a, magana ce ta cigaban kasa da al’umma da al’umma da kuma addini.
Wannan shi ne ya kamata, kodayake a mafi yawan lokaci mutane ba sa jin dadi a ce an fadi ra’ayi na gaskiya, saboda an fi son a dinga lallabawa. Shi kuwa maras lafiya ‘sannu’ ba ta warkar da shi; gara ka ba shi magani komai zafinsa, idan ya na cikin shan magani sai ka yi ma sa sannu ko bayan ya warke sai ka yi ma sa fatan alkhairi.
To, wajibi ne mu san wannan. Kodayake wasu lokuta abinda ya ke hana mutane su tsaya a yi gyara ko a zo da cigaba ko canji shi ne, idan mutane su ka dulmiya cikin abu daya, ya zamana cewa wani abu guda daya ya tara su, kowa ya na hadama a cikinsa ko ya shiga cikinsa ko kuma shi ma wannan laifin ya na yi ko barnar ya na samun riba a cikinta ko kamar yadda a ke cewa idan a na samun kudi a cikin laifi ko a na samun mukami ko mulki a cikinsa, to bai cika gyaruwa ta dadi ba.
Ko kuma kamar yadda a ka bada labari na cewa, wani limami, mamunsa su ka yi shawara a kan su daina bin sa sallah, saboda ya na neman mata. Don haka su ka yanke hukunci kawai idan ya zo sallah kada a bi shi. To, lokacin da limamin ya zo sallah, a al’ada idan liman ya taho a kan mike, to babu wanda ya mike. Ya shigo masallaci a ka ki tashi a yi ikama babu wanda ya kula shi. Ya ce a tashi a yi sallah, babu wanda ya kula shi. A karshe sai ya ce, ‘to ku meye dalilin da ya sa ba za ku tashi a yi sallah ba?’ Sai daya daga ciki ya ce, ‘saboda ka na neman mata. Don haka shi ya sa mu ba za mu bi ka sallah ba. Mu ka yanke shawara a kan haka.’ Sai Liman ya ce, ‘ah! ai kai na san wacce ka ke nema.’ Ya nuna wata ma ya ce, ‘kai ma na san wacce ka ke nema.’ Ya sake nuna wani ma ya ce, ‘kai ma na san wacce ka ke nema. Don haka sai ku tashi na ba ku sallah!’ Sai su ka tashi. Ka ga wato ba su da wata ta-cewa.
To, sau da yawa idan mutane su na jin dadin wata barna ko wata son zuciya, ba su cika son a zauna a ce za a kalli abinda ya kamata ba. To, wannan shi ne ya sa. Don haka ya zama wajibi ne a kanmu mu tashi mu tashi tsaye mu kalli wannan. Misali, idan mu ka dauki Arewa, za mu ga an gina ta ne a kan addini da siyasa. Duk jihohin Arewa za ka ga addini da siyasa ne, amma kamar jihar Kano an gina ta a kan addini da siyasa da kuma kasuwanci, kuma wannan ba a yi shi a banza ba, don wata manufa da wani tunani kuma za ka ga sau da yawa mutane Kano su ke koyi da ita a Arewa kuma ko a Najeriya Kano wata aba ce wacce ta ke alkibla ce.
To, ashe kenan ya kamata tun farko su kansu mutanen Kano su fara tunani na su samar wa kansu alkibla ta siyasa, alkibla ta jagorancin addini da alkibla ta wadanda su ke masu fada a ji. Duk da cewa, kungiyoyi na wayayyu na ’yan boko da na masu fada a ji sun yi yawa, amma dole ya zamana cewa a samu fahimtar juna. Ba za ka zo ka ce su narke su zama abu daya ba, saboda ba abu ne mai yiwu ba, amma ya zamana a tattaunawa da juna kan yadda yakamata a dora, ya zamana idan wani abu ya taso a rika yin abu tare. Amma idan ya zamana kowa gaban kansa ya ke yi kuma kowa ya na ganin shi ne kawai ya san mafita ko shi zai kawo mafita, to wannan ya na kara taimaka wa wajen abubuwa su lalace.
Wani lokaci akwai kwadayi da bukata ta son kai, wanda abinda hakan ya ke haifarwa shi ne son zuciya da rashin karbar gaskiya da rashin sanin abinda ya kamata, amma duk da haka ai ba kowa ne mai kwadayi ba kuma ba kowane wanda ya ke bukatarsa ta ke rufe ma sa idanu ba. Akwai mutane wadanda su ke da kishin wannan kasa Najeriya bakidaya kuma su ke da kishin Arewa kuma su ke yin kokari tukuru, domin su ga cewa kasar ta cigaba, amma babban cikas din shi ne, da zarar mutum ya fara, sai ka ga wadansu sun taso su na suka, su na aibata shi.
Su masu sukar nan ba za su iya yi ba, shi kuma wanda ya taso zai yi sun hana shi ya yi. Don haka har sai ya zamana mutum ya kasa ko kuma abu kadan daya taso duk sai a rarraba, a kama rigima. Wannan shi ne abinda ya kamata a yi shimfida a kansa.
Za mu ci gaba
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!