Connect with us

LABARAI

Za A Iya Rage Almajiranci A Arewa Idan Gwamnoni Sun Ware Kashi Biyar Na Kasafin Kudi – Farfesa Indo

Published

on

Wata Farfesa a Jami’ar Amadu Bello dake Zaria Aisha Indo Mohammed ta yi nuni da cewar, za’a iya magance Almajiranci a Arewacin Nijeriya ne kawai idan gwamnonin dake yankin suna ware kashi biyar bisa dari na kasafin kuzin su a duk shekara.
Indo ta bayyana hakan ne a jawabin ta a taron da kungiyar lillahi Charity da hadin gwaiwar Gudauniyar Womanhood suka shirya garin Kaduna.
Acewar ta, “ ya zama wajibi gwamnonin Arewacin Nijeriya su hada kansu don su dinga ware kashi biyar bisa dari na kasafin kudin su na duk shekara domin ta haka ne kawai za’a iya rage yawan Almajirancin a yankin”.
Ta bayyana cewar, ai suma gwamnonin a kwanan baya sun bayyana cewar, zasu bude tsagayoyi ga Almajiran dake a cikin jihihinsu don killace Almajiran.
Farfesar ta kuma koka akan yadda idan Almajiran suka kamu da nau’ukan rashin lafiya, Malaman nasu basa basu kulawar data dace.
Acewar ta, kashi tsa’in na Almajiran basa zuwa Asibiti idan basu da lafiya ko in sun kamu da wata cuta.
Ta bayyana cewar, lamarin na Almajiranci babban kalubale ne, musaman a yankin Arewacin Nijeriya, inda ta yi nuni da cewa, akwai misali karancin kudi, maganar samar da manhaja da za’a sanya darasun ilimin zamani don a dinga koyar dasu yaki da jahilci da kuma rashin bayar da horo ga Malaman na tsagaya.
Farfesa Indo ta kuma koka akan yadda Almajiran suke yin ragaita akan tituna don neman abincin da zasuci, musamman a tsakanin masu kananan shekaru.
Acewar ta, hatta sarakunan gargajiya suma basa goyon bayan Almajirancin, inda ta yi nuni da cewa, za kuma a iya magance yin Almajirancin ta hanyar yin amfani da sarakunan gargajiya da shugabannin alumma wajen yin gangami a birane da karkara da kuma samar da tsare-tsaren da suka dace.
Shima a nasa jawabin a gurin taron, Farfesa Abubakar Garba Suleiman daga Jami’ar NOUN a kasidar sa da ya gabatar ta mayar da hankali ne akan matsalar kiwon lafiyar Almajiran, yanayin wajen kwanan Almajiran da rashin sanun abinci mai gina masu jiki.
Ya yi nuni da cewa, shin iyaye, matakan gwamnati uku ko kuma alumma ne ya kamata su bayar da gudunmawa wajen rage Almajirancin a Arewacin Nijeriya, inda lamarin ya samo asali.
Ya yi nuni da cewa, idan daukacin alumomi zasu zage wajen bayar da goyon baya ta hanyar daukar dawainiyar Alamjiri daya don bashi ilimin boko, kula da lafiyar sa, suttura da kuma bashi abinci, matsalar zata ragu a Arewacin Nijeiya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!