Connect with us

MANYAN LABARAI

Dan Bindiga Ya Kashe Makiyayi A Kauyan Kaduna

Published

on

An bayar da rahoton kashe wani matashin makiyayi, wanda ake kira da, Mu’azu Jibo, a kusa da makarantar Sakandare ta gundumar Fadan Attakar, da ke karamar hukumar Kaura, Jihar Kaduna.

Da yake magana da manema labarai, shugaban kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah Cattle Breeders Association (MACBAN), ta kuduncin Kaduna, da kuma shugaban kungiyar ta Jihar Kaduna, Alhaji Abdulhamid Musa da Alhaji Haruna Usman Tugga, suka ce, abin ya faru ne da misalin karfe 11:00 na safiyar ranar Laraba, a lokacin da wani mutum dauke da bindiga ya budewa mamacin wuta, sannan ya gudu.

Abdulhamid Musa ya ce, dan bindigan wanda aka fi kiransa da, Taddius Nkom, an kama shi cikin dare daga baya, an kuma hannanta shi ga ‘yan sanda.

Shugaban kungiyar makiyayan, reshen Jihar Kaduna, Haruna Usman Tugga, ya yi kira ga makiyayan da ke yankin da su ci gaba da harkokin su, su kuma kasance masu bin doka, kar kuma su dauki hukunci a hannun su, domin jami’an tsaro a shirye suke su yi maganin duk wanda yake da hannu a aukuwan lamarin.

Duk kokarin da muka yi na jin ta bakin ‘yan sandan ya ci tura, domin Kakakin ‘yan sandan na Jihar Kaduna, DSP Yakubu Sabo, ba ya daukan waya, bai kuma maido da amsan sakwannin da muka aike ma shi da su ba, har zuwa lokacin kammala wannan rahoton.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!