Connect with us

LABARAI

Dubban ‘Yan Gudun Hijira Sun Samu Sabon Matsuguni A Jihar Borno

Published

on

Bayan gobarar da aka samu wanda ta haifar da asarar rayuka da na abinci da kuma na matsugunai a kwanakin baya a sansanin ‘yan gudun hijira. A yanzu an samar masu da sabbin matsugunai, wanda za su dauki dubban jama’a da za su zauna tare da samar da ci da sha da kuma kiwon lafiya da ma bangaren kula da koyarwa.

A shekarar bara, wannan sansanin yana dauke ne da jama’a kimanin mutum 8,600, amma aka kara fadada shi da isasshen guri inda yanzun aka raraba shi inda zai dauki mutum kimanin 300 aka fadada sansanin inda kimanin mutum 30,000 za su iya samun matsugunai.

A yanzun dai kimanin mutum dubu goma suke tsugune a wannan sabon gurin. Kuma ba a bukatar a tarar da cinkoso da zai hana samar da isasshen walwala da samun iska mai amfani ga al’umma mazauna wannan gurin.

An kuma tsara adadin mutanan da za su zauna a wannan sansanin da kuma abincin su da kuma tsaftaccen ruwan sha.

  Da yake jawabi a gaban dubban ‘yan gudun hijira, Malam Muhammad Goni ya ce; hukumar shiga da fice ta duniya ta sanya ido a kan sansanonin ‘yan gudun hijira saboda binciko gurbatattun da suke fakewa da sunan shiga sansanin ‘yan gudun hijira suna aikata ba daidai ba.

Ya ce; yanzun dai an samu nasarar tseratar da ‘yan gudun hijira dubu goma daga tsohon muhallin zuwa sabon muhalin, wanda yake da wadatacce da kyawun muhalli.

Shi ma a nasa jawabin, babban jami’in hukumar shigi da fice ta Duniya, Mista Robert Odhiambo ya ce; hukumar shigi da fice za ta kara tsaurara harkan tsaro da sanya ido a sansanonin ‘yan gudun hijiran saboda wani lokacin batagari suna shiga sansanonin da sunan su ma ‘yan gudun hijira ne, kuma su haifar da mumunar abu.

Kuma a sansanonin ‘yan gudun hijira a kan koyar da ‘yan gudun hijira abubuwan da za su yi ta fannin sana’o’i na dogaro da kai wanda zai taimakawa rayuwar su nan gaba.

Kuma Gwamnatin jihar Borno tana kara samar da matsugunan ‘yan gudun hijira mai rumfuna dari biyu.

Ya kara da cewa, kusan mutum milyan biyu ne ke rayuwa a sansanonin ‘yan gudun hijira sakamakon matsar rikicin Boko Haram a yankunan Arewa maso gabas.

Ya ce; mazaunan sansanonin ‘yan gudun hijiran akasarinsu cikin kashi tamanin mata ne da yara kanana, wadanda a koyaushe suna bukatar a taimakawa rayuwarsu.

Ya ce; dole mu hada hannu da masu arziki wajen taimakawa wadanan al’umman da suka kasance a wanan halin rayuwar su abin a taimaka ne. Kuma akalla ana bukatar milyoyin dalolin Amurka domin kara agaza masu da samar masu da abubuwan jin dadi da more rayuwa da zai rika kwantar masu da hankali su ji kamar suna gidajensu.

Rikicin Arewa maso gabashin Najeriya ya jefa al’umma cikin halin damuwa, wasu sun rasa danginsu wasu matan sun rasa mazajen su da yaran su.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!