Connect with us

ADABI

Gambo Mai Wakar Barayi: Shin Ko Ana Tuba Daga Aikin Adabi?

Published

on

Wannan tunani kusan haka ya kasance da Muhammadu Gambo mai waka barayi. Ban ji hirar da aka yi da Muhammad Gambo a Gidan rediyon da aka ce ya ce ya tuba da wakar barayi ba, sai dai ko kafin nan na saurari wadansu hirarraki, na kuma karanta wasu daga cikin wadand a aka yi da shi a bay,a kan wakokinsa da kuma yadda ba a son tattara wasu daga ciki, misali ta Inuwa Danmadacci da Tudu Tsoho. kamar yadda ya ce bai son tuna wannan gumurzu(tsakanin Inuwa da Tudu), tilas ta ya take rera wakar domin jama’a sun raja’ a a kan ta, duk kuwa da cewa ba a yi wannan gumurzu ba. Haka kuma wani dalilin da ya sa ya dade yana son barin waka bai wuce irin barayin da yake sha’awar yadda suke gudanar da rayuwar ta su a wancan zamani, yanzu sun kai ba sa sata irin ta da, ita ma yanzu ba ta; yanzu irin ta fashi da makami da daukar rai ita ce satar da yake gani; ba jarunta bare nuna fasaha da hikima don haka ya ce. ya bar bin wadannan barayi, sai dai rera wakokin da ya yi a fagage ko tarurrukan da aka gayyace shi.
Idan wadannan batutuwa suna daga cikin dalilan tuban Gambo daga wakar barayi yanzu, kila ga mai nazarin adabi ba zai ga laifinsa ba, domin ginuwar adabi na tafiya ne da muhallin da mai shirya adabin yake samun hasken gina adabin nasa. Idan yau a ce ba sarakunan gargajiya ko attajirai, yawancin mawakan Hausa za su rasa abin dafa wa, haka abin yake ga sauran sassan rayuwa. Ke nan barayi su ne rayuwar Gambo. Idan ba su to ba wakar barayi! Haka batun yake ga Gambo!
Ko Ana tuba aga aikin adabi?
Ni a tawa tsinkayar sai na ga idan an yi maganar tuba a Larabci ko a cikin harshen Hausa, ana nufin abin da aka yi baya ba kyau, ko dai ba dadi ko kuma ana nadamar aikata shi, amma shin haka batun yake a fagen adabi ko a gonar gina dabin? Ina jin ba batun tuba a harkar adabi, ke nan ba mu tsammanin mu samu wani abu wai shi adabi mai kyau ko adabin da bai da kyau. Haka batun yake a fagen nazarin ra’in adabi.
Ga mai son fahimtar yadda batun ya samo asali sai ya duba Eagleton(1983). A ra’in adabi, ba adabi mai kyau ko mara kyau, sai dai inda aka sanya son rai ko ra’ayi na mai nazari. Wannan ba ya nufin cewa ba za a iya samun ingantaccen rubutu ko rantsattsiyar waka ko burgaggen wasan kwaikwayo ko makamantan haka ba, ana yaba kyawon adabi, ana kuma yin yabon bisa wasu matattakalai da aka gindaya a cikn ra’in domin a bambanta tsakanin adabin da ke shiga zuci, cike da zakin saurare ko karantawa ko kuma kallo da kuma wanda yake mai lami, ko salaf.
Ke nan shirya da rera wakar barayi ba laifi ba ne, duk kuwa da cewa shi kan sa Gambo a wakar tasa yana ganin laifi ne. Ba muguwar aba ba ce kila shi ya sa, shi kan sa Gambo yake wa aikin adabin nasa lakabi da mugun kida, ba muguwar waka ba. Me ya sa muke wannan hasashe. Abin da aka riga aka sani ne yadda aka shata da kulla tunani a lokacin da ake wakar sarakuna ko attajirai ko malamai ko sauran jama’ar gari, haka ake yi a wakar barayi ko karuwai ko ‘yan daudu da makamantan su a cikin al’umma. Me ya sa wani zai yi tunanin wakar barayi a matsayin lalatattar aba ko maras kyau, alhali wakar noma ko ta sarakai ko attajirai wakar kwarai? Saboda sata muguwar sana’a ce, alhali sarauta ko noma ko malanta sana’o’in kwarai ne?
Mun yi wadannan tambayoyi ne domin muna danagaramar sanin kwaf ne, inda ake bayyana duk inda aka ga da a bayan mahaifiyarsa, a tambayi wane ne mahaifinsa. Bisa irin wannan karatu ne aka nuna mana cewa, adabi ‘hoto’ ne ko ‘madubi’, ke nan tun da mun san hoto ko madubi ba sa karya, ma’ana abin da ka hango ta amfani da madubi shi ne abin karaswa, haka abin da hoto da ke gabanka ya nuna maka a zahiri, haka abin yake, ashe adabi ba zai sharata ba. Idan ka yaga hoton don rashin jin dadi abin da ka gani ko ka fasa madubin domin ba ka son ganin abin da ka gani a ciki, ba zai canza lamarin ba. Saboda haka a matsayinmu na manazarta adabi abin da muka hango daga cikin wakar Gambo ta barayi, gaskiya ce, ko mu amince da haka ko mu ki! Ba yadda za mu yi mu canza batun, nan fa muna zance ne a fagen adabi ba wani fage can daban ba.
Mu sani ra’ayin jama’a, musamman na malaman addini ko na gwamnati ko na masu neman adaidaita tuanani a harkar adabi, ba zai canzawa adabin al’umma launi ba. Idan ka hana a sany wakar barayi a gidan rediyo, inda yawancin irin wadannn wakokin ake musu lakabi da NTBB ko hana a tattauna irin wannn adabi a makarantu ko wajen harkar ilimi, ba za ka hana wannan adabi gudana ba, shi ya sa muke ganin cewa, bisa tsarin ra’I na dabi, nan ba ra’ayi muke Magana ba, irin su Gambo da wakokinsa, tamkar malami da makaranta ne, fakat.
Daga dan binciken da na yim kan wannan fanni, sai na fahimci cewa yawancin irin wannan adabi, na batsa ne na sata ko na karuwanci ko na daudanci ko na bore ko na tarihin tashin-tashina, ana daukan sa a mtsayin karkataccen adabi, shi ya sa nakan tambayi kaina WA ko ME ya karkatar da shi, amsar da nakan ba kaina it ace ba wanda ya karkatar da irin wannan adabi face al’ummar day a samu kansa aciki, domin it ace ta samar da yabanyar da adabin ya rayu a cikinsa.
B awanna ba ma ai muna kuma sane da cewa, ita kan ta al’ummar ai kala biyu ce, ko dai wadda ke tafiya da rayuwar masu danniya ko kuma wadda ke janye da karikitan wadanda ake dannewa. A cikin wannan zubin rayuwar guda biyu ake samun adabawa da ke fike da kowane hannun riga guda, ko dai masu biyewa wadanda ke dannewa ko kuma masu agazawa wadanda ake dannewar(Gramaei,2005).
Wannan irin tunani ne Ngagi (1997) ya bayyana a matsayin wahalar da adabi ke ba hukuma ko ‘yan daidaito, ya kuma jaddada muhimmancin aikin adabi, ya damu da lalatattun al’amuran jama’a kodayaushe. Idan aikin adabi bai damu da irin wadannann lamuran ba,to da alama an yi haka da gangan ne, domin a ci gaba da danne al’umma. Irin wannan shi ya sa a zamanin wariyar launin fata a Afirka ta kudu aka yi ta watangaririya da marubuta irin su demis Brutus da Aled La Guma da Lewis Nkosi da wasu da dama. Wasu korarsu aka yi daga cikin kasar, wasu daure su aka yi, wadanda ba akora bas u bas u gudu ba, ko kuma ba a daure sub a, adabin su da rayuwar su sun kasance cikin tasku. Littattafan yawancin su an hana buga su, inda aaka samu aka buga an hana a karanta ko a sayar da su, saboda me suna fadar gaskiya! Me ya raba wannan tunani na masu wariyar launin fata da wanda aka yi ko ake yi wa adabin Gambo? Gambo ya sha dauri, ya tara. Ya sha bugu ya ga mune, duk saboda me ne? Albarkar mugun kidan nan! Za mu tsaya a nan sai mako na gaba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!