Connect with us

RAHOTANNI

Hanyoyin Da Manomi Zai Bi Domin Samar Da Iri

Published

on

Duk manomin da ke da samar da irin noma musamman a daidai wannan lokaci da damina ke kara karatowa, akwai wasu abubuwa da ya zama tilas ka sani, da za su baka haske a kan yanda ya kamata ka yi.
Hukumar samar da irin shuka ta kasa, wacce itace ainihin kungiyar da doka ta dorawa nauyin tantance irin shuka nagari da samar da shi gami da kasuwancin sa a cikin kasar nan, tana da wasu sharudda da ya zama tilas a cika su.
Na farko shi ne, a yi rajistar irin a wajen su domin tantancewa.
Zaban wajen da za a shuka irin wanda ya dace da shi ta yanda zai yi girman da ake bukata, tilas ne kuma a samar masa kebabben wajen da aka zaba masa daban da inda aka shuka sauran nau’ukan irin, kamar dai yanda masu tantancewa suka nuna, wanda zaka iya samun bayanin hakan daga hukumar tantancewar.
Da zaran an yi hakan, sai a shirya wajen da kyau domin samun ingancin sa, ta hanyar huda, kwakkwafewa da shirya shi kunya-kunya yanda ya kamata.
A tabbatar da an cire duk wasu shukokin da suke a filin ta hanyar fesa masu maganin fitar da ciyayi da yin kaftun filin domin fitar da duk kwayoyin ciyayin da suke a cikin kasa.
A tabbatar da an sami irin shukan ne daga inda ya dace (ana shawartanka da ka nemo irin shukan naka ne daga cibiyar da aka dora mata nauyin samar da irin shuka mai kyau ta kasa) ka kuma tabbatar da irin yana da nagartan da ake bukata.
Ka yafa shi ta hanyar da ta dace kamar yanda cibiyar ta nunamaka hanyar shuka iri nagartacce.
Kafin a girbe, a tabbatar da duk amfanin gonan ya bushe sosai. Kowace shuka a girbe ta daban da sauran, a tabbatar ba a cudanyasu ba a lokacin da ake adana su, kowane buhun shuka a yi masa tambarin sa daban da sauran domin a yi saukin gane su a lokacin da ake daukan su zuwa wani wajen ko kuma adana su.
Ka san abin da dokar samar da iri ta ce dangane da shi kansa irin.
Sashe na 17(1) na dokar samar da irin shuka yana cewa, babu wani mutum, baya ga wanda yake da rajista a karkashin dokar samar da iri da aka yarda ya samar da irin shuka, ko ya kasance yana yin aikin samar da irin ko yin kasuwancin sa. Ana karfafa shawartar manoma da su tabbatar da yin rajistan hakan tukunna.
“Laifi ne babba, a sayar, ko a yi nufin sayar da duk wani iri mai dauke da tambarin da ba na gaskiya ba, ko kuma wandaba shi ma da tambarin kala ko yanayin irin da ke cikin buhun, tilas ne a yi bayanin duk nau’in irin da yake kaumshe a cikin jakan kamar yanda sashen na 17(2), ya nuna.
“Duk wasu nau’ukan irin shuka da ake da nufin samarwa domin kasuwanci tilas ne su bi ta hanyar tantancewa kamar yanda dokar hukumar ECOWAS a kan irin shuka da dokoki da sharuddansa ta tanada.
Sashe na 17(3) ya bayyana cewa, “Sai dai kawai da manufar yin nuni, amma ba a yardan ma kowa ba ya je yana siyar da irin shuka a mazubin da yake budadde.
Sashe na 18(1) ya bayyana cewa, “Duk wani mazubin irin shuka tilas ne ya kasance dauke da tambari biyu, daya na hukumar tantance irin shuka, gudan kuma na ainihin wanda ya samar da irin. Shi na wanda ya samar da irin tilas ne ya kumshi bayanai kamar haka: sunan irin, kalarsa, lambarsa, yanayin sa da kuma nauyin sa, mafi karancin yanayin nunan sa, bayani a kan ko an yi wa irin magani ko ba a yi masaba, da kuma nau’in sinadarin da aka yi masa maganin sai adireshin wanda yake siyar da irin.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!