Connect with us

KIMIYYA

Sabuwar Fasahar Gano Wayar Da Ta Bata

Published

on

Wayarka na iya bacewa a kowanne lokaci, a saboda haka ya kamata ka kasance a cikin shirin yadda zaka bi sawu tare da gano wayar taka in aka sace. Wayar taka ko samfurin Smartphone Andriod ce ko kuma Tablet’ ya na da matukar mahimmanci ka tanadi daya daga cikin manhajar bin sawu tare da gano inda wayarka take, wadannan manhajar za su taimaka maka bin sawu tare da gano wayarka da ta bace, an yi wa wadannan manhajar jimillar suna ‘Android Debice Manager’.
Shafin Mash Tips ta bayyana cewa, akwai manhaja daban daban a rumbun ‘Google Play Store’ dake bayar da daman gano wayarka da zaran ta bace ba tare da wani bata lokaci ba, cikin wadannna manhajar a kwai na kyauta da kuma wadanda sai ka biya wasu kudade kafin ka iya amfani da su. Idan har kana da daya daga cikin wadanna manhajar a kan wayarka, za ka iya gano inda wayarka take kai tsaye a taswirar Google map, bayan ka shiga cikin account din daka bude daga kan kowanne kwamfuta kai tsaye. Wadanna manhajar na iya aika maka cikakken bayanan kiran da aka yi da wayar taka da kuma muryar wanda ya yi kiran da ma hoton barawon, bayanan za su tafi kai tsaye wani asusu daka bude wanda kuma ita za ka yi amfani da su wajen gano barawon tare da damke shi.
Ga wasu daga cikin manhajar da suka fi kyau, da za ka iya amfani dasu don gano wayarka ta Android. Wadannan manhajar na da karfin dawo da dukkan bayanan kiran da ka yi a baya da sakon karta kwana (SMS) da kuma sauran bayanan da suka shafe ka daga cikin wayar da aka sace maka don ka ci gaba da amfani da su. Manhajar na kuma da karfin gode dukkan bayanan dake a cikin wayar gaba daya musamman in ganowa tare da karbo wayar ta yi wuya.

Na farko shi ne ‘android debice manager’
A na samun wannnan manhajar ne a rumbun bayanai na Google, yana kuma taimakawa wajen gano wayar da ta bace ta hanyar kare dukkan bayanan dake a ciki.
‘Android Debice Manager’ yana taimakawa wajen gano wayarka ta hanyar Google account’ dinka, zaka kuma iya sake jerin lambarka na sirri da kake amfani das u wajen bube wayar ka kuma goge dukkan bayanan dake a kan wayar gaba daya daga duk inda kake.

Na biyu kuma shi ne ‘abast anti-theft’
Wannna manhajar dai kyauta ake samunta a rumbun bayanai na google, yana kuma taikamawa wajen bin sawu tare da gano wayar a aka sace. ‘Abast Anti-Theft app’ na amfani ne da taswirar google map wajen bi sawu tare da kuma amfani da fasahar GPS wajen gane takaimaimai inda wayar take don mai shi ya dauki matakin karbar wayar tasa.
Za kuma a iya amfani da wannna manhajar wajen sarrafa waya daga nesa, ana kuma iya aika sakon karta kwana zuwa ga shafin masu manhajar na musamman mai suna http://my.abast.com., inda sukan yi amfani da bayanan sirri da suke das hi na wayar wajen kullewa tare da goge dukkan wani bayanai dake a cikin wayar gaba daya. A na kuma iya amfani da wannan manhajar wajen sauraran bayanai dake fitowa daga wajen da wayar take tare kuma da daukan hotunan wrurin da wayar take, dukkan wadannan bayanan na iya taumakawa wajen gano inda wayar take tare da wanda ya saceta. Manhajar na kuma iya amfani da bayanan katin wayar na SIM card don taimakawa a gano inda wayar take, shi kuma wannnan manhajar na iya boye kanta a cikin waya ba tare da an akwaita a ciki ba, saboda kada barawon ya yi maza maza ya goge daga cikin wayar gaba daya.

Na hudu shi ne ‘prey anti-theft’
Wannnan manhajar na kare waya daga sharrin barawo, yana kuma bin sawu tare da gano dukk inda aka boye waya da sauran na’u’rori irinsu Tablets da Laptop. Manhajar ta taimakawa wajen gano duk inda na’urar taka yak eta hanhar fasahar ‘geo-location’ kyauta kuma ake samun manhajar a rumbun bayana da Google, da zaran ka bude asusunka na gmai.

Na biyar kuma shi ne ‘cerberus anti-theft’
Wannnan manhajar na bayar da kariya kai tsaye ga dukkan bayananka dake a cikin wayar da aa sace har zuwa lokacin da ka kai ga ganowa tare da karbe wayar taka daga hannun barawon. Ana iya samu daman amfani da manhajar na gwaji na tsawon mako daya, daga baya kuma ana iya ci gaba da amfani da manhajar har abada bayan ka yi biya sau daya.
Wannna manhajar na hanyoyi uku wajen kare wayarja daga sharrin barayi, na farko shi ne ta shafinsu na www.cerberusapp.com, ana kuma iya sarrafa wayar da hanyar sakon karta kwana wanda nan take sakon zai kai ga wanda yake amfani da wayar koda ya sanya wani sabon Sim card ne a cikin wayar, wannnan hanyar na taimakawa wajen sarrafa wayarka daga duk inda kake haka kuma a duk inda take, yana iya gano daidai inda wayar take tare kuma yin kara na musamman koda kuma wayar na a cikin tsarin nan ne na yin shiru ‘Silent Mode’.

Bitdefender Daga karshe kuma akwai ‘Anti-Theft Bitdefender’
Wannnan manhajar na kullewa tare da kuma goge dukkanin bayanan dake a kan wayarka da ta bace a dukk lokacin da kake bukata a kuma du kina wayar take ba tare da bata wani lokaci ba. wannnan manhajar na da wani tsari na musamman dake kare dukkan bayanan dake cikin wayar daga duk wani katsalandan daga wanda ya saci wayar, don kuwa a kwai ani tsari na musamman dake hana shiga ko kuma goge dukk abin dak a kan wayar har said a izini daga ainihin mai wayar.
Dukk da wadanan manhajar na iya taimaka maka ganowa tare da dawo da wayarka da aka sace, yana da magukar kyau ka yi kokarin kare dukiyarka daga sharrin barawo, don kuma masu iya Magana sun ce, kula da kaya yafi ban cigiya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!