Connect with us

SIYASA

Shekara 36 Da Rasuwar Malam Aminu Kano: Abubuwan Da Za A Jima Ana Tuna Shi Da Su

Published

on

Ranar 17 ga wata hudun shekara ta 2019 ce ta kasance ranar da tsohon dan gwagwarmaya mai kishin talakawa Malam Aminu Kano ya cika shekata 36 da mutuwa, a irin wannan rana kamar kowace shekara an shirya taron karawa juna sani tare da bujiro da wasu kyawawan abubuwan alhairi na dan kishin kasar kuma jagoran talakawa Malam Aminu Kano.
A wannan rana an gudanar da taruka iri daban-daban a Cibiyar harkokin Demokaradiyya da ke Gidan Mumbayya wanda nan ne tsohon Gidan Marigayi Malam Aminu Kano kuma nan kabarinsa yake, a lokacin taron shehunnan malamai daga Jami’ar Bayero da sauran bangarorin harkokin ci gaban kasa
suka gabatar takardu tare da fadakarwa
Cikin wadanda suka gabatar da Jawabai alokacin bikin tunawa da cikar Malam Aminu Kano shekara 36 da rasuwa akwai tsohon shugaban kungiyar Lauyoyi Na Nijiriya Barista Abubakar Balarabe Mahmoud wanda ya bayyana damuwarsa bisa matsalar tsaro da kasar nan ke fuskanta wanda
ke barazana ga siyasarmu da kuma tattalin arzikin Kasar nan.
Ya ce, musamman Arewacin kasarnan da kuma Nijeriya baki daya, dole sai shugabanni da sauran masu ruwa da tsaki sun mayar da hankali wajen fuskantar wannan kalubale wanda ke kokarin kassara makomar Kasar nan.
Shima tsohon alkalin alkalan Jihar Kano yace akwai matsalar gazawar gwamnatoci ta fuskar tunkarar matsalar dake addabar kasarnan, musamman ya ce akwai gazawa ta fuskar kananan shari’u da kuma rashin ingancin tsarin gudanar da shari’a, don haka sai ya bukaci a yi gaggawar samar da kwaskwaarima a tsarin shari’a matukar ana fatan kawo karshen matsalar tsaro da kuma amfanar tsarin demokaradiya mai ma’ana.
Shi ma ana sa Jawabin Mai Martaba Sarkin Kano Malam Muhamamd Sanusi II ya kalubalanci masu ruwa da tsaki acikin harkokin gudanarwar Kasar nan, ciki kuwa har da Shugaban sashin tsaro, bangaren shari’a, Malamai, Sarakunan gargajiya, shugabannin al’umma da kafafen yada Labarai, inda
yace kowanne dayansu na jin tsoron abinda zai same shi idan ya fadi gaskiya. Ya ce Sarki yana jin tsoron fadin gaskiya kan rashin adalcin da gwamnatoci ke shiryawa domin gudun kar a tsige shi, haka al’amarin
yake ga kafafen yada labarai, bangaren shari’a da Malamai.
Ya ce dole sai mun sake tunani akan haka, in ji Sarkin.
Malam Muhamamdu Sanusi II yace matukar muna son samun ingantacciyar al’umma, dole sai mun zama cikin shirin sadaukar da kai tare da fuskanatar duk wani sakamako da ka iya biyo baya. Dole sai mun cire tsoro daga zukatanmu, idan kuma ba haka ba zamu tabbata cikin rashin adalcin shugabanni bisa biyan bukatun son zuciyarsu, ya ce kasar nan na cikin wani hali na gibi a shugabanci inda a wasu wuraren babu doka da oda.
Shima Mataimakin shugaban Jami’ar Bayero dake Kano Farfesa Yahuza Bello wanda mataikin shugaban Jami’ar bangaren mulki ya wakilta Farfesa Haruna Wakili ya jinjinawa cibiyar Mumbayya bisa jajircewa
wajen ci gaba da gudanar da wannana muhimmin taro na tunawa da Malam Aminu.
Ya ce Jami’ar Bayero nayin duk abinda ya kamata wajen tabbatar da ganin an fito da kyawawan ayyukan gwarazan shugabanni domin zama wata fitila ga shugabannin masu zuwa domin tabbatar da ciyar da kasar nan gaba.
Takaitaccen Tarihin Malam Aminu Kano An haifi Malam Aminu Kano daga zuriyar Malam Yusif wanda gogaggen malami ne daga gidan Gyanawa na Fulani, mahaifinsa ya kasance Muhutin Alkali ne a kotun Jihar Kano.
Ya Halarci makarantar Kwaleji dake Katsina, kafin ya wuce zuwa Jami’ar London tsangayar ilimi tare da
Marigayi Abubakar Tafawa Balewa. Ya samu shaidar takardar Malanta bayan kammala karatunsa a Katsina wanda alokacin kuma ya zama malamin Makaranta wanda ya fara koyarwa a makarantar horar da malamai da ke Bauchi.
Tun a lokacin da Malam Aminu Kano ke Bauchi ya samu damar tattauna batutuwan siyasa ta yadda ya fadada harkokin siyasa da kuma fannonin ilimi wanda ya wuce matsayinsa na malamai, a lokacin ya rubuta wata makala mai taken Kano a kakarshin Gudumar shugabannin lardi, sannan
kuma alokacin suna tare da Tafawa Balewa sun kansace mamba a kungiyar ci gaban hadin kan Bauchi, har ila yau shi ne sakataren Da’irar tattaunawar Jihar Bauchi. Ya zama shugaban Malamai na cibiyar horarwa ta Maru da ke Jihar Sakkwato a wancan lokacin, sannan ya zama sakataren
kungiyar Malaman Arewa.
Jamhuriyya ta Farko Lokacin da yake Sokoto ya zama mamba a Jam’iyyar Mutanen Arewa, sai
kungiyar al’adun arewa wadda daga baya ta narke ta zama jam’iyyar siyasa NPN, a shekara ta 1950 ya jagoranci wani bangare na Jam’iyyar Mutanen Arewa inda suka kafa Jam’iyyar NEPU, wanda kafin haka wani dan kabilar Inbira dan Kasuwa Mai suna Habib Raji na da wata Jam’iyyar mai suna NEPA a Jihar Kano Haka kuma an kafa wata sabuwar Jam’iyyar wadda Malam Aminu Kano tare da wasu ‘yan kishin kasa irinsu Magaji Dambatta, Abba Maikwaru da Bello Ijumu wadanda ake jin duriyarsu aduk wata harkar siyasar lardin Arewa.
Wadanan mutane sun hada karfi wajen yakar matsalar murdiya da danne hakin talakawa wadda shugabannin lardin arewacin Nijeriya suka shahara a shekara 1951, a lokacin jam’iyyar tasu ta shiga takarar zaben fid da gwani wanda kuma akalla suka samu nasara, bayan kafuwar Jam’iyyar NPC ne kuma Malam Aminu Kano ya fara fuskantar Kalubale musamman a zabuka biyu na majalisun tarayya. A shekara 1954 Malam Aminu Kano ya fadi zaben wakilin majalisar wakialai ta tarayya wanda
Maitama Sule ya samu Nasara da kuma shekara 1956. Malam Aminu Kano bai samu nasara ba sai a shekara 1959 inda ya samu nasarar lashe zaben karkashin tutar Jam’iyyarsa ta NEPU wanda wannan nasara ta ba shi damar zama mataimakin mai tsawatarwa a Majalisar wakilan.
Bayan Juyin Mulkin da sojoji suka yi ne ya kawo karshen mulkin demokaradiyyar Jamhuriyya ta farko, Malam Aminu Kano ya yi aiki da gwamnatin Mulkin soja wadda Janar Yakubu Gawon ke shugabanta a
matsayin Kwamishinan ma’aikatar lafiya.
Jamhuriyya ta biyu, bayan shafe shekara 12 sojojin na mulkin Nijeriya a watan satunmbar shekara ta 1978 sojojin suka dage takunkumin siyasa wanda hakan ya sa aka kafa jam’iyyu biyar wanda suka hada da NPN,UPN, da sauran guda ukun wanda Jam’iyyar PRP da malam Aminu Kano, Sam Ikoku da Edward
Ikem Okeke ke jagoranta, jam’iyyyar ta samu goyon bayan kungiyar ma’aikata irinsu Michel Imoudu, a 1979 Jam’iyyar PRP ta tsayar da Malam Aminu Kano a matsayin wanda zai mata takarar shegabancin kasa wanda akarshe bai samu isasshiyar kuri’un da zasu kaishi ga lashe zaben ba, amma dai Jam’iyyar PRP ta samu nasarar samun Kujerar Gwamnoni biyu, Kano da Kaduna.
Malam Aminu Kano na cikin ‘yan siyasar Arewa da ake girmamawa kwarai da gaske, wanda ya tabbatar da tsarin ingantacciyar siyasa mai cike da adalci, Aminu Kano ya haifar da tsarin tallafawa mata da ‘yancin fadin albarkacin baki.
Domin tunawa da kyawawan nasarorinsa an sawa muhimman wurare sunansa wanda suka hada da filin sauka da tashin jiragen sama na Kano, Makarantu, tituna da asibitoci. Yanzu haka kuma gidan da ya
rayu acikin, ya kuma mutu acikinsa sannan kuma aka bizne acikinsa an mayar da shi cibiyar gudanar da binciken harkokin siyasa da horarwa wanda ke karkashin kulawar Jami’ar Bayero da ke Kano abokan Gwagwarmayarsa Alhaji Alasan Dawaki na cikin sauran abokan gwagwarmayar siyasar malam
Aminu Kano, alokacin da yake tattaunawa da manema Labarai kan muhimman abubuwan da za a jima an tuna Malam Aminu Kano dasu, ya bayyana cewa Ko shakka babu babban abin da Malam Aminu Kano ya tsana shi ne Zalunci da danne hakkin talaka, sai kuma yadda ya yi gwagwarmaya wajen wayar
da kan talakawa domin su san akasu. Yace Malam Aminu Kano na cikin mutane da suka wayar da al’umamr arewa kai wajen shiga aikin soja, domin kafin wannan kokari na sa gani ake aikin soja aiki ne iskanci kawai.
Yace Malam Aminu Kano ya samu kyakkyawar tarbiyya ne daga Mahaifinsa wanda shima gogaggen malami ne, sai kuma Malamin shi kansa Malam Aminu Kano wanda duk inda Malam zai yi wani jawabi yakan nanata ambaton sunan malaminsa Malam Bello Kano da kuma Madaki Shehu.
Ya ce abokan gwagwarmayarsa a siyasance sune irinsu Owolowo, Azikwe da sauransu.
Alhaji Alasan Dawaki ya nuna takaicinsa bisa yadda ahain yanzu cikin siyasar wanan lokaci babu batun akida, domin acewarsa alokacin da suke siysa da Malam Aminu Kano ba wanda ake baiwa ko sisin kobo, wasu awaki da tukaminsu suke sayarwa domin halarta tarukan jam’iyya, amma yanzu da talakawa da masu neman mulkin kowa ba abinda yake tanada da ya wuce kudi, wannan tasa idan suka hau kujerun mulki babu maganar akida.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!