Connect with us

KASASHEN WAJE

Tsohon Shugaban Benin Ya Gargadi Shugaba Talon

Published

on

Tsohon Shugaban Jamhuriyar Benin Boni Ya yi bgaragadi Talon lokacin da ya gana da manema labaren kasashen Duniya domin sanar da su halin da kasarsa ke ciki da kuma bayyana takaicinsa ga salon siyasar Shugaban kasar mai ci Patrice Talon.
Ranar 28 ga watan Afrilun nan ne za a gudanar da zaben yan Majalisu ,wanda ga baki daya hukumar zaben kasar ta soke takardun jam’iyoyi masu adawa da Shugaban kasar.
Wannan lamari ya soma haifar da tashin hankali a wasu sassan kasar musaman arewacin kasar Benin.
Shugaban kasar Patrice Talon a baya, ya bayyana cewa ya yi iyakacin kokarin sa don gani an shawo kan wannan matsalla ,sai dai bangaren yan adawa sun kaucewa zaman tattaunawa na kawo karshen rikicin da ya kuno kai tsakanin su.
Tsohon Shugaban kasar Boni Yayi ya bayyana damuwa matuka da cewa yanayin siyasa da kasar ta fada zai iya haifar da tashin hankali mudin Shugaban kasar Patrice Talon bai dau matakan da suka dace don bai wa ‘yan adawa damar shiga zaben kasar ba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!