Connect with us

LABARAI

Bikin Easter: Akalla Mutum 100 Suka Mutu A Wani Harin Bam A Sri Lanka

Published

on

Wadansu bama-bamai da suka tashi a wadansu gidajen kwana guda uku da aka sani da Otel da wasu Cocin kasar Sri Lanka sun haddasa mutuwar mutane da dama a birnin Colombo na kasar Sri Lanka. Rahotanni sun nuna cewa; sama da mutum 100 ne a yayin da sama da mutum 200 suka jikkata a harin.

Wadannan hare-hare sun gudana ne a lokacin da kiristoci a Sri Lanka ke gudanar da addu’oinsu dangane da tunawa da ranar da suka yi amannan an bayar da Isa Almasihu domin a gicciye shi.

Akalla sama da mutum dari ne ya zuwa hada wannan rahoton aka tattance sun rasa rayukan su, yayin da sama da dari biyu aka garzaya da su asibiti inda ake ci gaba da kawo wadansu har yanzu. Lamarin ya wakana daf da gidan Firaministan kasar .

 

.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!