Connect with us

MANYAN LABARAI

Buhari Ya Nuna Takaicinsa Kan Rikicin Taraba Da Adamawa

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana takaicinsa a akan rikicin da ya addabi kabilar Jukun da Tibi a jihar Taraba da kuma na Fulani da Genjon da kuma kabilar Bachama na jihar Adamawa abin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama da kuma jikkata dubbai.
Shugaba Buhari ya bayyana haka ne ta bakin babbana jami’i mai bashi shawara a kan harkokin watsa labarai, Malam Garba Shehu, a sanarwar da ya raba wa manema labarai a Abuja jiya Asabar.
Ya ce, ”Tashin hankali da zub da jini ta kowanne hanya abu ne da ba za a amince da shi ba ta kowanne hanya, musamman a wannna lokacin da ake bukukuwan Ista a fadin kasar nan, duk kuwa dimbin darussa da wannna lokacin ke koya mana na zaman lafiya da juna ba tare da nuna bambamci ba.
”Tashin hankali ba zai taba sama hanyar maganin rashin fahintar da muke fuskanta ba a tsakanin mu na mutane.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kuma yi kira na a gagauta kawo karshen rikicin tare da samar zama lafiya a fadin jihohin gaba daya.
Ya ce, gwamnati za ta nemi a tattauna a tsakanin dukkan masu ruwa da tsaki don gano usabbabin rikicin da nufin kawo karshen rikicin gaba daya.”
Haka kuma shugaban kasar ya kuma bukaci Malamam addini su gaggauta samar da hadin kai da zama lafiya a tsakanin dukkan bangarorin dake tashin hankali a jihar filato da Kaduna da Taraba da kuma Adamawa.
”Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kuma umurci hukumar NEMA da sauran kungiyoyin bayar da agaji su kai dauki ga mutanen dake fuskantar matsananciyar matsaloi a sakamokn rikicin.
”Shugaba Buhari ya kuma bukaci gaggauta samar da sojoji ayankin dopn samar da zama lafiya da gaggawa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!