Connect with us

LABARAI

Zan Gina Jami’a Na Sa Mata Sunan Mijina- A’isha Buhari

Published

on

Matar shugaban kasa, Aisha Buhari, ta bayyana cewa; tana son samar da jami’a mai zaman kanta wacce za ta sanya wa jami’ar sunan mijinta ‘Jami’ar Muhammadu Buhari’. Matar shugaban kasar ta bayyana hakan ne a jiya Asabar a wani taro da ta shirya tare da hadin guiwar ‘yan asalin jihar Adamawa wanda ya gudana a garin Yola.

A’isha wacce ba ta bayyana inda za ta gina jami’ar ba, ta bayyana cewa; za ta gina jami’ar ne tare da hadin guiwar kasashen Sudan da Katar. A’isha ta koka bisa yadda ake fuskantar a matsalolin a bangaren ilimi da sauran bangarori a kasarnan. Inda ta yi kira da smaun hadin kai da goyon bayan ‘yan asalin jiharta domin cimma muradin gwamnati.

 

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!