Connect with us

RAHOTON MUSAMMAN

Nan Da Shekara Biyar Matasa Za Su Iya Hana Mu Fita – Dangote

Published

on

Babban dan kasuwar nan wanda ya fi kowa kudi a Nahiyar Afrika, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana cewa, akwai yiwuwar nan da shekara biyar matasan jihar Kano marasa aikin yi su iya hana manyan jihar fita ko da kofar gida ne saboda barazanar da za su iya zama.
Dangote ya bayyana haka ne a lokacin gudanar da gagarumin taron cigaban jihar Kano, wanda kungiyar samar wa da jihar alkibla ta KCCI ta shirya ranar Asabar da ta gabata.
Ya kara da cewa, “yadda Allah ya hore wa kasarmu ta Najeriya filin noma har kashi 75 na kasar, to bai kamata a ce mutanenmu su na cikin talauci ba. Don haka dole ne mu tashi tsaye wajen bunkasa harkar noma da masanaantu, domin su ne manyan hanyoyi fitar da kasa daga talauci yadda za ta samu cigaba. Kamar yadda kasashen duniya su ka dauki matakai su ka ciyar da kasashensu gaba, to mu ma haka ne ya kamace mu yi. “
Ya ce, “irin abubuwan da su ke faruwa ya nuna haka, kamar shekara daya da rabi da ta wuce na je sallar Juma’a a Abuja na yi shiga ta doguwar riga, wacce da yawa mutane ba sa gane ni sabanin irin shigar da saba yi ta babbar riga, amma sai wani matashi ya kyalla ido ya ce ga Dangote. Kafin lokaci kadan matasa sama da dubu sun rufe ni. Da kyar na shiga mota. Don haka dole mu dauki matakin sama wa matasa aikin yi.”
Haka kuma Dangote ya ce, “ba wani shugaba ko wani gwamna da za mu zaba wanda ba zai yiwa al’umma aiki ba, kuma dole ne wannan tafiya mu kira gwamnoninmu, musamman na Arewa mu gaya mu su gaskiya, mu tunkari wannan kalubale gabadaya.”
Haka kuma Dangote ya sha alwashin shi da dan kasuwa dan uwansa Alhaji Abdussamadu Isiyaka Rabiu za su gina katafariyar cibiyar koyar da sana’o’i, don amfanin matasa maza da mata a Kano, za kuma su gina titi mai tsawon kilo mita tara wanda ya lalace a Sharada, wanda za su yi amfani da kudin harajinsu da su ke biya, kamar yadda a ka cimma yarjejeniya a hukumance da kuma bada tallafin biliyoyin Nairori, “don ciyar da jihar nan gaba kamar yadda ni Dangote da BUA mu ke da kudirin haka.”
Shi kuwa mai masaukin baki kuma shugaban tsangayar DBS da ke jami’ar Bayero, Farfesa Murtala Sabo Sagagi, tunda farko sai da ya bayyana muhimancin daukar matakan yakar talauci da bunkasa tattalin arzikin kasa sakamakon karuwar al
umma na kasha 3.3 cikin 100 wanda ke nufi duk shekara 20 mutanen Kano za su ninka yawansu.
Shi kuwa Alhaji Kabiru Sani Kwangila Yakasai (SKY) ya bayyanawa ’yan Jarida cewa, “wannan taro cigaba ne. Tunda manya sun zo yin gyara alamar sun fara jin matsalar rashin tsaro da tabarbarewar tattalin arziki a tare da su, to alamar gyara ya zo kenan. Tunda manya su ka fara daukar matakan gyara abin a yaba mu su ne kuma kowa ya bada gudunmawarsa kamar yadda ya kamata.”
Shi ma Alhaji Salisu Sambajo ya bukaci matasa su daina raina sana’a, inda hakan ke jawo ’yan kauye su yi kudi, dan birni na cikin talauci.
Daga karshe shugaban KCCI, Alhaji Bashir Othman Tofa, ya bayyana wannan taro da wannan kungiya ta samu nasara idan a ka yi la`akari da maganganun da a ka tattauna da kuma burin da a ke da shi na kawar da dukkanin matsaloli da ke kawo wa Kano da kasa koma-baya.
“Wannan babbar nasara ce ga mutanen Kano da kasa,” a cewar tsohon dan takarar shugaban kasar.
Shi kuwa Hon. Abdullahi Haruna Yari Bori ya shaida wa wakilinmu fatan cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi koyi da kasar China wajen bunkasa ilimi da raba al’ummar Najeriya da bakin talauci.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!