Connect with us

KASASHEN WAJE

Ya Datse Yatsansa Kan Takaicin Yin Zaben Tumun Dare

Published

on

Wani mutum ya datse yatsansa manuniya a kasar Indiya, a bisa takaicin zaban Jam’iyyar da ba ita ya so ba a babban zaben kasar Indiya.
Pawan Kumar, ya sami rudani ne a kan alamomin Jam’iyyun, don haka sai ya mannawa Jam’iyyar, Narendra Modi’s party, a maimakon Jam’iyyar hamayya ta yankin su na Jihar Uttar Pradesh, a ranar Alhamis, kamar yanda dan’uwansa ya yi bayani.
Kumar, dan shekaru 25, ya garzaya gida ne ya nemi wukar da suke yanka nama da ita a gidan na su, inda nan da nan ya datse yatsan na shi da ita.
Duk da cewa, ana yin zaben ne ta hanyar na’urar zabe ta zamani, amma dai akan dauki hoton yatsa manuniya da tawada bayan yin zaben, domin tabbatar da wanda ya yi zaben bai sake zuwa wani waje ya dangwala kuri’ar ba.
“Cikin zumudi yake, ganin wannan shi ne karo na farko da zai yi zabe,” in ji dan’uwan na shi mai suna, Kailash Chandra.
Chandra ya ce, iyalan na su sun yi hanzarin kai Kumar Asibiti.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!