Connect with us

MAKALAR YAU

Bola Ahmad Tunubu: Sarka Mai Rikicin Rikirkita Najeriya (II)

Published

on

Idan aka lura a cigaba da kokarin da Bola Ahmad Tunubu yake na rikirkita Najeriya to alamu na nuni da cewa ragamar tafiyar da shugabancin Muhammadu Buhari a karo na biyu zai rika tafiya ne a hannun Tunubu.
Alamu na farko da suke nuna haka shi ne, shi kad ai ne mutun a Najeriya kuma a cikin jam’iyyar APC yake da mutanen da ko shugaba Buhari baya da su kuma ko yana da su ba su da karfi fad a a ji a gwamnatin kamar mutanen Bola Tunubu.
Muna kallon yadda a dalilin kamfanoninsa da ke bakar cuwa-cuwa a hukumar kula da sha’anin inshorar kafiya (NHIS) wanda sabon shugaban wajan Farfesa Usman Yusuf ya iske ana sheke aya da kud ad an ‘yan Najeriya amma daga ya d auki matakin hanawa wanda saboda haka a kawo shi karshe dai yanzu an koreshi kuma daga jihar Katsina ya fito.
Farfesa Usman Yusuf ya fad i irin bad akalar da ake yi a wannan hukuma wanda ko gwamnatin shugaba Buhari bata sani ba sai bayan ya zo wajan, daga karshe dai ya kare a kora wannan mutumin Buhari ne kuma anyi masa shaida irin ta buhari cewa mutumin kirki ne, saboda su Bola suna da hannu a cikin lamarin har zanga-zanga aka rika yi masa a hukumar.
Idan muka koma batun shugaban hukumar masu yi arzikin kasa ta’anati watau EFCC Malam Ibrahim Magu mun ga yadda aka rika yin jeka ka dawo da majalisar dattawa ta kasa da kuma bangaran zartarwa akan maganar tantance shi ya zama shugaban hukumar mai cikakken iko.
Ibrahim Magu wad anda suka san siyasar Najeriya sun fad a cewa Bola Ahmad Tunubu shi ya kowa shi saboda cimma wata manufa ko dai yanzu ko kuma nan gaba, amma saboda d aurin gindin Tunubu gashi har yanzu ba a tantance shi ba kuma ba a sauke shi ba.
Masana suka ce, dokar kasa ta bayyana cewa duk mutumin ya da wuce wata shida yana rikon kwarya akan wani mukami a gwamnatince kuma ba a tabbatar da shi ba a matsayin shugaba mai cikakken iko, to dole ya sauka ya bar wannan hukuma amma ya ya Magu ya bar hukumar EFCC?
Ko ta halin kaka wanda ya kawo shi yana son sai ya kai inda yake so, batun a cire shi ko a canza shi sai dai idan wanda ya kawoshi ne yake da bukatar hakan, amma abin da wahala wai a dafa kaza a yada.
‘ya ‘yan jam’iyyar APC na halas sun yi kuka har sun gaji saboda irin d abi’ar rashin ganin mutuncin d an adam da shugaban Jam’iyyar APC Adam Oshemole yake nuna masu amma saboda Bola Tunubu ya kawo sai dai idan mutuwa za su yi su yi, har yanzu babu wata hanyar ta yin maganin wannan matsala, ko ba su da hakkin ne oho!
Yanzu Adams zai iya taka wanda yake so, ya yi abinda yake so, ya fad i abinda yake so, saboda kawai yana yaron Bola Ahmad Tunubu, bayan haka kuma idan ya ga dama ya haddasa rigima a jam’iyyar da yake shugabanci amma ba zaka taba jin an ja hankalisa ba domin ya gyara. Wai wace irin kasa muke ne kuma wad anne irin shuwagabanin muke da su?.
Saboda Adams ya nuna cewa shi isashe ne, cewa yake ba za su sake yarda wani daga jam’iyyar PDP ya rike wani mukami a majalisar dattawa ta kasa ba, kai ka ce ba su da hakkin yin hakan, alamu na nuna cewa akwai abinda aka shirya shi yasa aka turo Adams domin ya fara isar da sako, nan gaba kad an kawai mai sakon na nan zuwa.
Kodayake wannan magana ba zata taba zama abin mamaki ba domin kuwa kwana kwana nan ne ubangida nasa ya bayyanawa zababbun ‘yan majalusa cewa duk wanda ba zai zabi Ahmad lawan ba ya bar jam’iyyar ka ji rainin wayau, ba fa shugaban kasa bane yake fad in wannan magana ba, a ‘a su Bola Tunubu ne masu mulkin Najeriya a boye.
Haka kuma duk da irin zafin da ake cewa shugaba Muhammadu Buhari yana da shi na rashin yadda ayi ba dai dai ba, sai da Bola ya nuna masa cewa indai akan sa ko kuma wani na shi to abin ba haka yake ba, munga alama sai dai ace Allah Ya kiyaye gaba.
Kwamitin da shugaban kasa ya kafa akan yin binciken tsohon sakataran gwanatin tarayya Babachir Lawal ya bada shawara a koreshi amma sai da ‘yan Najeriya da ake ganin ba su isa ba sun fara magana sannan aka ga Buhari ya yi abin nan da ake cewa ihu bayan hari ya korashe ba tare da hukuntawa ba.
Da wuta ta yi wuta, shi ne daga karshe aka ce a gabatar da Babachir Lawal a gaban kuliya manta sabo bisa zarginsa da yin ba daidai ba a lokacin da yake sakataran gwamnatin tarayya, wannan fa bayan kowa ya fitar da ran cewa doka zata iya aikin akan yaron Bola Tunubu kuma tuni ‘yan Najeriya suka fara dawowa daga rakiyar shugaba Buhari akan wannan na batun cin hanci da rashawa.
Wannan fa duk sun faru ne saboda Bola Tunubu shi ne ya kawo Babachir a matsayin sakataran gwamnatin tarayya, kuma Allah ka d ai yasan yadda aka yi har shugaba Buhari ya d auki wannan matakin akanshi domin kuwa wannan mutumin ya fi karfi a yi masa haka saboda yana da uwa a gindin murhu, kuma ba don gudun Allah ya isan ‘yan Najeriya ba da Buhari bai ce uffan ba akan Babachir lawal.
Yankin arewa ya zama abinda ya zama ya yi wata irin suma wada sai dai ace Allah ya kawo wanda zai cece yankin arewa amma ba dai a wannan gwamnati ba da Yarabawa suka fi kowa shanawa da morewa ba, amma kuma su ne koma baya wajan samar da kuri’un da suka ba Buhari dama sake zama shugaban kasa karo na biyu.
To wai idan aka cigaba da tafiya haka ina wannan yanki na arewa zai koma, babu wani muhimmin abu da aka kawo a karkashin wannan gwamnati duk wani aiki sai dai aji cewa ya tafi yankin yarabawa saboda su Bola Ahmad Tunubu sune da gwamnati
Wani ubangidana a jarida wanda yanzu yana aiki a matsayin Edita a wata jarida da ke Abuja ya fad a mani cewa in rubuta in ajiye idan shugaba Buhari ya ci zabe a 2015 sai su Bola Ahmad Tunubu sun yi wa Buhari kawanya (Cage) na dad e ban gane abinda yake nufi da haka ba sai daga baya na fara fahimatar cewa ashe anyi gwamnati wanda bahaushe ke cewa kura da shan bugu gardi da amshe kud i ce…
Wani abun ban takaici shi ne yadda wad anda ake kira da dattawan arewa suka zuba ido suna ganin yadda Bola yake juya wannan gwamnatin amma sun yi shiru sun kasa cewa komi alhali kullin yankinsu ake nunawa ana cewa sune gaba wajan talauci da yunwa da fatara da rashin tsaro da satar jama’a da rashin ilimi da rashin harkar kiwon lafiya da sauransu.
Wai a haka don Buhari ne ke mulki, muke ganin haka yanzu duk ranar da ake ce yau babu shugaba Buhari ya arewa da ‘yan arewa za su kasance,? wani abin ban haushi da takaici shi ne yadda mafiyawan ‘yan majalisar dattawan da aka zaba daga arewa yanzu suke ta ruguguwar yi wa Bola biyayya akan bakar manufarsa ta kumsawa ‘yan Najeriya shuwagabannin majalisar da su Bukola Saraki sun fi kima da daraja nesa ba kusa ba.
Yanzu idan haka ta tabbata shikenan mun kara komawa hannunsa sai dai abinda Allah ya yi, amma dai ya kamata tun yanzu a fara neman mafita domin ko ba komi akwai ‘yan baya wad anda anan gaba za su tambayi yadda aka gudanar da shugabanci a wannan lokaci kuma za su so jin labarin wannan annobar da ta sami arewa a dalilin san ran Bola Ahmad Tunubu amma ba ya son ‘yan arewa sai dai su yi masa zabe ya ci moriyar abinsa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!