Connect with us

KASUWANCI

FAAC Ta Rabar Da Naira Tiriliyan 1.92 Ga Matakan Gwamnati Uku A Farkon Zango Na 1 Na 2019 —NBS

Published

on

Rahotan da Hukumar Kididdiga ta Kasa NBS, ya sanar da cewa, Kwamitin asusun tarayya FAAC, ya rabar da naira tiriliyan 1.92 ga matakan gwamnatin uku a zangon farko na shekarar 2019.
NBS ta sanar da hakan ne a cikin rahoton na FACC na kuzin da aka rabar na watan Jabairu, Fabirairu da kuma Maris na shekarar 2019.
Adadin na rabar da kudin da NBS ta wallafa a kafarta ta yanar gizo a ranar Litinin data gabata a Abuja NBS taci gaba da cewa, FAAC ta rabar da naira biliyan 649.19 ga matakan gwamnati uku a Janairun 2019; sai naira biliyan 660.37 a Fabirairu, sai kuma nair biliyan 619.86 a Maris.
Daga cikin naira tiriliyan 1.92 , Gwamnatin Tarayya ta samu naira biliyan 803.18, Jihohi naira biliyan 530.14 sai kananan hukumomi naira biliyan 398.43.
Fashin bakin ya nuna Gwamnatin Tarayya ta samu naira biliyan 270.17 a Janairu sai naira biliyan 275.33 a Fabirairu da kuma naira biliyan 257.68 a Maris.
Jihohi sun samu naira biliyan 178.04 a Janairu sai naira biliyan 182.17 a Fabirairu sai kuma naira biliyan 169.93 a Maris.
Kananan hukumomi kuwa, sun samu naira biliyan 133.83 a Janairu sai naira biliyan a Fabirairu 136.88 sai kuma naira biliyan 127.72 a Maris.
NBC tace, adadin da aka rabar a Janairu idan aka kwatanta da naira biliyan 547.46 da suka fito daga asusun SA na naira biliyan 100.76 an tara tane daga harabin BAT, inda naira miliyan 976.53 daga nudin musaya da aka samu riba.
Naira biliyan 45.36, an rabawar da jihohi masu albarkatun man fetur, a matsayin kaso kashi 13 da ake basu
Hukumomi masu tara nudin shiga kamar Kwastam, FIRS da DPR, sun samu naira biliyan 4.69 , N4.04 da naira biliyan da kumma naira biliyan 8.04 a matsayin ribar su ta nudaden da suka tara.
A karin fashin baki akan rabon da Gwamnatin Tarayya ta samu ya nuna cewa naira biliyan 216.57 an zuba su a cikin asusun Gwamnatin na tafa kudi.
An raba nudin dauki na musamman naira biliyan 4.81 da kuma naira biliyan 2.43 na Gidauniyar kare muhalli.
An kuma rabar da naira biliyan 8.15 don ciyar da ma’adanai da kjma naira biliyan 5.82 ga babban birnin tarayya Abuja.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!